Yadda Budurwa Ta Hada Shagalin Murnar Haihuwarta, Amma Kawayenta Suka Yi Zuwa

Yadda Budurwa Ta Hada Shagalin Murnar Haihuwarta, Amma Kawayenta Suka Yi Zuwa

  • Shagalin murnar haihuwar wata budurwa ya zama zama mata taron kuka yayin da ta gayyaci jama'a suka ki zuwa
  • Wani bidiyo ya shafukan sada zumunta ya nuna yadda aka kayata dakin taro da nufin yin shagalin, amma kuma bakin da suka hallara
  • Jama'a da dama a intanet sun yi martani, sun bayyana murnarsu daga nesa tare da nuna mata kauna duk da ba sa tare

Wata matashiya mai shekaru 18 ta zaman zugum yayin da ta yi bikin cika shekara amma babu wanda ya hallara.

Mutane da dama sun nuna kauna da taya ta shagalai ganin yadda aka kowa ya guji zuwa wurin wannan shagali.

Budurwa ta kadu, ta hada biki babu wanda ya hallara
Yadda Budurwa Ta Hada Shagalin Murnar Haihuwarta, Amma Kawayenta Suka Yi Zuwa | Hoto: TikTok/@talitha.ci.okolo
Asali: UGC

Wata mata da tace 'yar uwar budurwa mai shagalin ne ta yada bidiyo a TikTok, ta nuna yadda dakin shagalin ya kasance babu kowa a ciki.

Hakazalika, bidiyon ya nuna daki-daki na zagayen kayataccen dakin taron da ya kwalliya tare da tulin abinci a kan tebur amma ba mai ci.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mutum biyu da aka nuna a bidiyon su kadai ne suka hallara, kuma su ma din su ke da komai na bikin.

Duk da cewa Legit.ng Hausa bata iya tantance gaskiyar ikrarin matar na cewa babu wanda hallara ba, amma dai bidiyon ya nuna alamun babu kowa.

Kalli bidiyon:

Martanin 'yan TikTok

thiscrownischerished yace:

"Ga shi kuma ta yi kyau, ki hakuri yarinta, ubangiji na nan kuma shi ya hana mutanen da ba za su amfane ki ba zuwa."

Chi ta ce:

"Sam yarinya wadannan ba kawayenki ne na arziki ba matukar dai basu ba, ki yi hakuri da faruwar hakan.

kachi yace:

"Ba zai yiwu ba! ta yaya kike tunanin kina da kawayen da za su shirya dakin taro haka? ??!.!"

VIPROOM yace:

"Wayyo Allah idan dai wannan ba wasa bane ina matukar baki hakuri, da kin gayyace mu da mun cika wurin."

wh0s.cheryl yace:

"Ban yarda gaskiya wannan bidiyon kafin fara taron ne kawai saboda wa zai ki zuwa ci da shan jalof da kayan sanyi da kuma rakashewa da waka?

Shikira Johnson yace:

"Yarinya da na yi kudin jirgi daga Burtaniya, ki yi gayyatar kasa da kasa a nan gaba.

Miji Ya Tasa Matarsa a Gaba, Yana Mata Dariya Yayin da Take Girki da Gawaye a Madadin Gas

A wani labarin, wani dan Najeriya ya jawo cece-kuce a kafar sada zumunta ya yin da ya yada bidiyon matarsa na girki da murhun gawayi.

A wani gajeren bidiyo da @ismailamzat01 ya yada a TikTok, an ga mutumin na kyalkyalewa da dariyar mugunta yayin da matar ke girki.

A cewar mutumin, yana dariya ne saboda akwai lokacin da ta dage cewa ba za ta taba amfani da murhin gawayi ba, amma gashi ta tsinci kanta a amfani dashi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel