Wani Yaro Mai Shekaru 10 Ya Nutse a Tafki a Jihar Jigawa

Wani Yaro Mai Shekaru 10 Ya Nutse a Tafki a Jihar Jigawa

  • Hukumar tsaro ta NSCDC ta bayyana mutuwar wani yaro mai shekaru 10 da ya tafi ninkaya da abokansa a yankin jihar Jigawa
  • An tsinci gawarar wata yarinya a bakin hanya a karamar hukumar Hadejia, hukumar na ci gaba da bincike a kai
  • A daminan bana ne mutanen jihar Jigawa suka gamu da iftila'in ambaliyar ruwa, an yi asarar dukiyoyi da rayuka da dama

Jihar Jigawa - Mun samu labarin cewa, wani yaro mai shekara 10 ya nutse a ruwa a karamar hukumar Buji ta jihar Jigawa a ranar Asabar 26 ga watan Satumba.

Kakakin rundunar hukumar tsaro ta NSCDC a jihar Jigawa CSC Adamu Shehu ne ya tabbatar da hakan a ranar Lahadi a birnin Dutse, Daily Trust ta ruwaito.

Yadda wani yaro ya nutse a tafki a jihar Jigawa
Wani Yaro Mai Shekaru 10 Ya Nutse a Tafki a Jihar Jigawa Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) cewa, yaron ya tafi wanka ne a wani dan tafki da ke kauyen Lelen Kudu tare da wasu abokansa sai kawai shi tasa ta zo karshe.

A kalamansa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“An gano gawarsa awanni biyu bayan ya nutse, kuma likita ne ya tabbatar da mutuwarsa."

Ya ce nan take aka dauki gawar aka mika ta ga iyayen yaron tare da yiwa iyayen gargadi da su daina barin 'ya'yansu suke zuwa ninkaya a tafki ko kogin da ya tumbatsa.

An tsinci gawar wata yarinya a Jigawa

Hakazalika, ya ba da labarin yadda hukumar ta gano gawar wata yarinta a gefen hanya a karamar hukumar Hadejia ta jihar, rahoton jaridar Premium Times.

Ya ce an gano tsinci gawar ne a ranar din da ta gabata a unguwar Kandahar da ke karamar hukumar.

Ambaliyar Ruwa Ta Tashi Al'ummar Garuruwa Sama da 10 a Jihar Jigawa

A wani labarin kuma, labarin da muka samu daga jihar Jigawa a arewa maso yammacin Najeriya ya nuna cewa aƙalla ƙauyuka 11 ruwa ya lalata a ƙaramar hukumar Ringim.

Shugaban ƙaramar hukumar, Honorabul Shehu Sule Udi, shi ya faɗi haka yayin wata hira da manema labarai a sasanin 'yan gudun Hijira da ke garin Ringim.

Yace matsanancin ruwan ya barnata yankunan kana ya tilasata wa mutanen da ke zaune a ciki yin ƙaura daga gidajensu, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel