An kama sojan gona da kayan hukumar FRSC dauke da katin shaidar aikin soja a Kano
- An kama wani mutum mai suna injiniya Gude Ude dauke da kayan hukumar FRSC har ila yau dauke da takardan sheda na soji
- Jami'an hukumar FRSC da kewaye a titin Kaduna-Kano ne sukayi kachibus dashi kuma bayan sun gane dan damfara ne suke cafke shi
- Daga bisani sun kai shi ofishin yan sanda na Kumbotso kana aka gurfanar dashi gaban wata kotun majisatre a Kano domin ya fuskanci hukunci
Jami'an hukumar kiyaye hadura na kasa (FRSC) da hukumar yan sanda sun kama wani mutum mai suna Injiya Gude Ude a jihar Kano da kayan jami'an hukumar kiyaye hadura FRSC kuma dauke da katin shaidar aikin sojan a garin Kano.
Sanarwan da hukumar FRSC ta bayar mai dauke ta sa hannun mukadashin Secta Kwamanda, Ahmed T. Mohammed ta cean kama Ude ne a ranar Alhamis, 4 ga watan Janairun 2018 a titin Kaduna - Kano a yayin da rundunar ke gudanar da wata kewaye na musamman da akayi wa take da "Operation Zero"
DUBA WANNAN: Rikicin APC a Kano: Wata kungiya ta bukaci hukuma ta bincike Abbas
Sanarwan ta kuma bayyana cewa Ude yana tuka mota ce kirar Sharon mai lambar rajista MKA 269 HU. Bayan an dakatar dashi ya yi ikirarin cewa shi jami'in hukumar FRSC ne kuma an same shi da kayan jami'an hukumar ta FRSC.
Da aka lura cewa sojan gona yake yiwa hukumar ta FRSC, sai aka cafke shi kuma daga bisani aka tafi dashi ofishin yan sanda da ke Kumbutso kana daga baya aka gurfanar dashi gaban kotun majistare da ke addreshin mai lamba 47 layin kotu a Kano.
Ganin haka ne yasa hukumar ta FRSC ta ke gargadi da al'umma da su rika lura da yan damfara da ke amfani da sunan hukumar wajen zambatar masu mota da sauran abubuwan hawa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng