So Ajali: Ummita, Bilyaminu da Wasu Mutane da Masoyansu Suka Kashe Kan So

So Ajali: Ummita, Bilyaminu da Wasu Mutane da Masoyansu Suka Kashe Kan So

Masana a fannin soyayya na cewa kasancewa da wanda kake so yanayi ne mai daɗi da ya zarce kwatance amma duk daɗin so, wani lokacin ta na zuwa da tashin hankali ko ajali.

Daily Trust ta tattaro cewa irin haka ta faru a Kes ɗin wata matashiya Ummukulsum Sani Buhari (Ummita) a Kano, a baya-bayan nan masoyinta ɗan China ya yi ajalinta.

Lamarin ya shiga jerin adadin abubuwan tashin hankali da suka faru, inda ake samun abokan tarayya na rasa rayuwarsu a hannun waɗanda suke ƙauna.

Lamarin Ummita da Ɗan China.
So Ajali: Ummita, Bilyaminu da Wasu Mutane da Masoyansu Suka Kashe Kan So Hoto: dailytrsut
Asali: Twitter

Legit.ng Hausa ta tattaro muku wasu daga cikin irin haka da so ya zama Ajali.

Ummita

Bayan kace-nace da dogon labari kan makasuɗin kashe Ummukulsum, wacce saurayinta ɗan China ya aikata, da yawan mutane sun ayyana kazamin lamarin da so mai sarƙaƙiya, kulawa, ɗaukar fansa da zubar jini.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A ranar 17 ga watan Satumba, 2022, wani Ɗan China ya shiga har ɗakin Ummita yar kimanin shekara 23 a gidan iyayenta dake Janbulo, ƙaramar hukumar Gwale a birnin Kano inda ya daɓa mata wuka har lahira.

Bayanai sun nuna cewa Mamaciyar, wacce aka ce ta taɓa aure, tana soyayya da mutumin kuma tsawon shekaru suna tare. Da yawan mutane sun ce ɗan China ya aikata wannan ɗanyen aiki ne saboda an ci amanarsa.

Maryam Sanda

A watan Nuwamban shekarar 2017, wani lamarin kisan kai da mata ta aikata kan mijinta ya ja hankalin mutane. Yan sanda sun kama Maryam Sanda bisa zargin halaka mijinta, Bilyaminu Haliru Bello a Abuja.

Marigayi Bilyaminu, ɗa ne ga tsohon shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Dr. Muhammed Halliru Bello. Sai dai Maryam ta musanta tuhumar kisa da aka jingina mata.

Ta faɗa wa Kotu cewa a ranar 18 ga watan Nuwamba, 2017, ta ɗauki wayar sahibinta domin ta yi kira amma sai ta gano Hotunan wata budurwa tsirara. Nan take ta sauka daga Bene domin su fahimci juna da mijinta.

A cewarta, yayin da suka fara musayar yawu kan lamarin wanda ya haddasa kardama mai zafi, ta nemi marigayin ya sauwake mata. Lamarin ya ƙara muni da yammacin ranar.

Maryam tace, "Ya ture ni yayin da faɗi ƙasa na fasa kwalbar Shisha bisa kuskure kuma ruwan dake ciki ya watse a tsakar ɗakin. Ana haka na jiyo ɗiyarmu na kuka, na nemi ya barni naje na duba ta."

Maryam ta ƙara da cewa yayin da Bilyaminu ke kokarin riƙe ta sai ya faɗi ƙasa bisa rashin sa'a kwalbar nan da ta fashe ta soki ƙirjinsa.

Tun da jimawa Kotu ta yanke wa Maryam Sanda hukuncin kisa amma ta ɗaukaka ƙara zuwa Kotun ƙoli.

Yewande Oyediran

A ranar 27 ga watan Nuwamba, 2017, Babbar Kotun jihar Oyo ta yanke wa wata lauya, Yewande Oyediran, hukuncin zaman gidan gyaran hali na shekara 7 bisa zargin daɓa wa mijinta wuƙa har ya mutu.

Mataimakiyar Datakta a ma'aikatan shari'a ta jihar Oyo, Yawande, an tuhumeta da daɓa wa mijinta, Lowo Oyediran, wuƙa yayin da wata gardama ta haɗa su.

Rahoto ya nuna cewa ta aikata masa wannan ɗanyen aiki da ya yi ajalinsa a gidansu dake Adeniyi Layout, Abidi-Odan, Akobo, Ibadan jihar Oyo ranar 16 ga watan Fabrairu, 2016.

Barista Udeme

Haka zalika, wata Lauya mai suna Udeme, ta soka wa mijinta, Otike Odibi, wuƙa har yace ga garinku nan a watan Mayu, 2018. Lamarin ya faru da karfe 7:30 na safe a Anguwar Diamond Estate, Sangotedo, jihar Legas.

An ruwaito cewa Barista Udeme ta yanke mazantakar mijinta da wuƙa kana ta damƙa masa ita a hannunsa na dama.

Folashade Idoko

Folashade Idoko, ma'aikaciyar lafiya wato Nas, ta shiga hannun 'yan sanda bisa zargin ɗaba wa mijinta, Lawrence Idoko, wuƙa har lahira a gidansu da ke Ayetoro, yankin Oto-Awori jihar Legas saboda zargin yana neman mata.

An ce Folashade ta kalubalanci marigayi mijinta ne da neman mata a waje, wanda hakan ya haddasa rigima tsakaninsu har mai aukuwa ta auku.

A wani labarin kuma Ɗan China Ya Bayyana babban dalilin da ya tunzura shi har kashe masoyiyarsa Ummita a jihar Kano

Geng Quangrong, ɗan asalin ƙasar China mazaunin Kano da ya kashe wata budurwa ya magantu kan dalilin aikata kisan.

A ranar Jumu'a, Deng, wanda bayanai suka nuna suna soyayya da Mamaciyar, ya kutsa har gida ya daɓa mata wuƙa har lahira.

Asali: Legit.ng

Online view pixel