Tashin Hankali: Wani Kwamishina Ya Tsallake Rijiya da Baya a Jihar Nasarawa

Tashin Hankali: Wani Kwamishina Ya Tsallake Rijiya da Baya a Jihar Nasarawa

  • Yan bindiga sun buɗe wa tsohon kwamishinan muhalli wuta a jihar Nasarawa amma ya tsallake rijiya da baya
  • Musa Ibrahim Abubakar, ɗan takara a inuwar NNPP mai kayan marmari, ya faɗi yadda ya tsira da raunukan harbi a harin
  • Shugaban ƙaramar hukumar Doma, Ahmad Sarki, yace tuni aka kai rahoton lamarin ga hukumar yan sanda

Nasarawa - Kwamishinan muhalli da ma'adanai da bai jima da sauka daga muƙaminsa ba a jihar Nasarawa, Musa Ibrahim Abubakar, ya tsallake rijiya da baya a harin 'yan bindiga.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa a baya-bayan nan Mista Abubakar ya fice daga jam'iyyar APC bayan shan kaye a zaɓen fidda gwani na fidda yan takarar majalisar jiha.

Musa Ibrahim Abubakar.
Tashin Hankali: Wani Kwamishina Ya Tsallake Rijiya da Baya a Jihar Nasarawa Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Bayan ficewa daga APC, tsohon kwamishinan ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar NNPP mai kayan marmari inda ya karɓi tikitin takarar mamba mai wakiltar mazaɓar Dama ta kudu a majalisar dokokin Nasarawa.

Kara karanta wannan

"Ba Kuskure Bane" Jam'iyyar APC Ta Faɗi Dalilin Sanya Jigon PDP a Kamfen Tinubu, Ta Maida Martani Ga Gwamnoni

Da yake labarta yadda ya tsallake harin ga yan jarida yayin da yake jinya a Asibiti, Abubakar yace:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Ina cikin raɗaɗi, amma ina son bayyana wa duniya cewa a ranar 21 ga wannan watan, na je garin Rukubi na raba kayan tallafi da suka haɗa da tsabar kuɗi ga mutanen da Ibtila'in ambaliya ta shafa a ƙaramar hukumata, Doma."
"Bayan gama aikin, na kama hanyar komawa gida a garin Doma, ba zato wasu 'yan bindiga kusan 9 suka buɗe mun wuta ta kowane ɓangare. Harsashi ya same ni ta gaba wayar salula ta kare, wani ya same ni a kafaɗa da baya na."
"Harsasai 46 aka harbi motata da su, lamarin ya faru da karfe 5:30 na yamma a kusa da ƙauyen Igbabo, kusan kilo mita 20 zuwa garin Doma. Ina da yaƙinin waɗanda suka farmake ni manyan yan siyasa ne a wata jam'iyya."

Kara karanta wannan

Rikicin APC: Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan Na Gab Sanin Makomarsa a 2023

Ta yaya tsohon kwamishinan ya tsira?

Da yake ƙara bayani kan lamarin, tsohon kwamishinan yace lokacin maharan da masu nufin kashe shi ke cigaba da harbi sai ya ƙara gudu da motarsa a kokarin tsere musu.

Yace yana cikin tafiya kawai motar ta tsaya yana gab da shiga ƙauyen Igbabo, daga nan ya samu ya fice da gudu yana kuruwar neman taimakon mutane.

A cewarsa, wasu mutanen kirki suka taimaka suka ɗauke shi a Babur zuwa garin Doma, daga nan ya wuce Asibirin Ɗalhatu Araf Special Hospital dake Lafiya, babban birnin jihar.

Tsohon kwamishinan ya gode wa Allah bisa taimakon da ya samu daga mutane, waɗanda suka yi amfani da tufafi wajen ɗaure raunukan da ya ji don kar ya rasa jini da yawa.

Yace ya kwashe kwanaki uku a Asibibin ana kulawa da shi, daga baya kuma ya canza wani Asibitin mai sirri saboda tsaro.

Wane mataki hukumomi suka ɗauka?

Kara karanta wannan

Bello Turji Ya Fusata, Ya Yi Magana Kan Harin da Jirgin Yaƙin Soji Ya Kai Mafakarsa a Zamfara

Shugaban ƙaramar hukumar Doma, Ahmad Sarki Usman, yace lokacin da ya samu labarin ya kaɗu kan yadda 'yan bindiga ke farmakan mutane ana gab da zaɓe. Yace an sanar da yan sanda lamarin.

Duk wani kokari na jin ta bakin hukumar 'yan sanda bai kai ga nasara ba kasancewar Kakakin reshen Nasarawa, DSP Rahman Nansel, ya ƙatse kiran salular da aka masa.

A wani labarin kuma Sojoji Sun Harba Manyan Makamai Kan 'Yan Ta'adda, Da Yawa Sun Zarce Lahira

Dakarun sojin Najeriya sun harba makamai masu haɗari kan mayaƙan kungiyar ISWAP bayan samun bayanan sirri a Yobe.

Rahoton Zagazola Makama ya nuna cewa tulin 'yan ta'addan sun rasa rayukansu sakamakon samamen sojin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel