Jami’an tsaro a Najeriya sun yi shekara ba su gano Abubakar Dadiyata ba

Jami’an tsaro a Najeriya sun yi shekara ba su gano Abubakar Dadiyata ba

A karshen makon nan ne aka cika shekara guda cif da yin gaba da wani Matashi, Abubakar ‘Dadiyata’, wanda ya yi suna wajen sukar gwamnati mai mulki a Najeriya.

A ranar 1 ga watan Agusta, 2019, wasu mutane biyu da ba a san su wanene su ba, su ka shigo har gidan Malam Abubakar Idris, su ka dauke shi, har yau babu labarin halin da ya ke ciki.

An dauke Abubakar Idris wanda aka fi sani da ‘Abu Hanifa’ ko ‘Dadiyata’ ne a gidansa da ke Kaduna, aka cusa shi cikin motarsa, a gaban iyalinsa Khadijah Ahmad Lame.

Daga wannan lokaci babu wanda ya sake jin labarin Dadiyata, ko ya ga motarsa ko kuma ya yi nasarar tuntubar layin wayar salularsa. Iyalinsa da danginsa su na cikin matukar bakin ciki.

Dadiyata wanda malamin jami’a ne a Najeriya, ya auri Sahibarsa, Khadijah Ahmad ne shekaru bakwai da su ka wuce, kuma su na da ‘ya ‘ya mata biyu – Hanifa da kuma Fatima.

Hanifa mai shekaru bakwai ta kan matsawa mahaifiyarta game da labarin mahaifinta, har yau ba ta san amsar da za ta bada ba. Fatima kuwa karamar yarinya ce mai shekaru kimanin biyu.

Da aka yi hira da mai dakin wannan Bawan Allah, cikin tsananin takaici, ta ce ba ta san ta inda za ta fara ba. Amma duk da haka ta na yi wa mijin na ta addu’a a fito da shi lafiya.

KU KARANTA: Kwankwaso ya bukaci DSS ta fito da Dadiyata

Jami’an tsaro a Najeriya sun yi shekara ba su gano Abubakar Dadiyata ba
Abubakar Dadiyata Hoto: Twitter/Dadiyata
Asali: Twitter

"Hanifa ta kan tambayi ‘yaruwarta: “Ko kin ga Abba? Ina nemansa ne kurum!”

Malam Dadiyata mai kusan shekara 35 ya na cikin masu sukar kura-kurai da barnar gwamnatin tarayya, jam’iyyar APC da mala’un Najeriya a kafafen sada zumunta musamman Twitter.

Matashin ya yi karatun Digirinsa na farko da na biyu ne a jami’ar Bayero da ke Kano da kuma wata jami’ar kasar waje, a lokacin da aka sace shi, ya na kokarin karatun PhD a ketare.

Jami’an DSS wanda ake zargi da yin caraf da Abubakar ‘Dadiyata’, sun tabbatar da cewa ba ya hannunsu. ‘Yan Sanda kuma su na ikirarin su na kokarin kubutar da shi.

Jama’a da kungiyoyi da ‘yan siyasa irinsu Rabiu Musa Kwankwaso, Femi Fani-Kayose, da Shehu Sani su na cigaba da kira ga jami’an tsaro su kubutar da wannan Bawan Allah.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng