Mataimakin Shugaban Kasa, Osinbajo Ya Dira Jihar Kano Don Ta’aziyyar Rasuwar Dan Sanata Gaya

Mataimakin Shugaban Kasa, Osinbajo Ya Dira Jihar Kano Don Ta’aziyyar Rasuwar Dan Sanata Gaya

  • Mataimakin shugaban kasan Najeriya, Yemi Osinbajo ya kai wata ziyarar ta'aziyya jihar Kano a Arewacin Najeriya
  • Ya kai ziyarar ne gidan Sanata Kabiru Gaya da ya rasa dansa a cikin makon nan kamar yadda rahotanni suka tabbatar
  • Gwamnan Kano ne ya karbi Osinbajo a filin jirgin sama, ya kuma mika godiyarsa ga mataimakin shugaban kasar

Jihar Kano - Daily Trust ta ruwaito cewa, mataimakin shugaban kasan Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya kai ziyara jihar Kano don yin ta'aziyyar rasuwar dan sanata Kabiru Gaya da ya rasu a makon nan.

Osinbajo ya ce Sadiq Gaya, da ga sanatan kamar da yake a wurinsa, inda ya bayyana jimamin rashinsa.

Daga nan ne Osinbajo ya bayyana ta'aziyyarsa da ban hakuri ga iyalan sanatan bisa babban rashin da suka yi, rahoton Channels Tv.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Mance Da Batun Tinubu, Ya Fadi Wanda Zai Sa Ya Gaji Buhari Da Yana Da Iko

Osinbajo ya kai ziyara Kano
Mataimakin Shugaban Kasa, Osinbajo Ya Dira Jihar Kano Don Ta’aziyyar Rasuwar Dan Sanata Gaya | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Da yake bayyana jimaminsa Osinbajo ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Wannan ziyara ce mai matukar ban takaici. Sadiq matashi ne. Kamar da yake a wurina. Ya ziyarce ni sau da yawa. Lauya ne shima kamar dai ni. Don haka, ina da alaka mai karfi dashi.
"Na yi matukar ji wannan rashin. Ina mika ta'aziyyata ga ga sanata da dukkan iyalansa, gwamnati da al'ummar jihar Kano bisa wannan rashi da wannan da mai matukar daraja."

Kanawa na godiya

A bangarensa, gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da tun da farko ya tarbi mataimakin shugaban kasan a filin jirgin sama, ya gode masa bisa wannan karimci.

A cewarsa:

"Ba wannan ne karon farko da ka zo ba, ka zo a lokuta da dama, Mun gode kuma Allah ya yi maka albarka."

A nasa martanin, mahaifin Barista Sadiq, Sanata Gaya ya nunawa Osinbajo iyalansa, kana ya mika godiyarsa ga mataimakin shugaban kasar bisa wannan ziyara

Kara karanta wannan

2023: Tsohon Kakakin Majalisar Tarayya, Ghali Na'Abba, Ya Sauya Sheka Zuwa PDP, Ya Fallasa Sirrin APC

Da yake yaba halin dansa, sanatan ya ce ziyarar ta Osinbajo ta sake shajja'a ahalinsa, kuma yana kara mika godiyarsa.

Allah Ya Yiwa Dan Sanata Kabiru Gaya Rasuwa a FCT Abuja

A wani labarin, dan majalisar dattawan Najeriya mai wakiltan mazabar Kano ta kudu, Sanata Kabiru Gaya, ya yi rashin daya daga cikin 'yayansa.

'Dan masu suna Sadiya Kabiru Gaya, ya rasu ne ranar Talata 13 ga Satumba kuma an yi jana'izarsa da yamma bayan Sallar La'asar a birnin tarayya Abuja.

Marigayin ya kasance Lauya da hukumar manajin dukiyoyi watau AMCON dake Abuja. Hussaini Ambo Indabwa, Mai magana da yawun mahaifinsa Sanata Kabiru Gaya, ya sanar da hakan ga manema labarai a Kano, rahoton Leadership.

Asali: Legit.ng

Online view pixel