Rayuwata Na Cikin Hadari Tun Bayan Yiwa Sarauniyar Ingila Elizabeth II Mummunan Fata, Farfesa Uju Anya

Rayuwata Na Cikin Hadari Tun Bayan Yiwa Sarauniyar Ingila Elizabeth II Mummunan Fata, Farfesa Uju Anya

  • Farfesa 'yar Najeriya Uju Anya dake koyarwa a jami'ar Amurka, ta bayyana barazanar da take fuskanta tun bayan yin mummunan fata a Twitter ga Sarauniya Elizabeth ta II.
  • Anya ta kuma zargi Jeff Bezos, mai kamfanin da tunzura jama'a akanta tare da kawo wa rayuwarta tsaiko
  • Farfesar ta ce ba ta amfani da shafin Facebook, amma maganganu na ta yawo a kafar cewa tana goyon bayan kungiyar IPOB da sauran kungiyoyin ‘yan aware

Farfesa 'yar Najeriyar nan dake zaune a Amurka da ta yi fatan mutuwa mai radadi ga sarauniyar Ingila ta bayyana cewa, rayuwarta na cikin matsanancin hali.

Uju Anya farfesa ce a sashen Harsunan Zamani a Jami’ar Carnegie Mellon ta kasar Amurka, in ji jaridar The Punch.

Rayuwar farfesar da ta kullaci sarauniyar Ingilana cikin hadari
Rayuwata na cikin hadari tun bayan yiwa sarauniyar ingila mummunan fata, farfesa 'yar Najeriya | Hoto: @UjuAnya
Asali: Twitter

Meye Anya ta yi haka?

Farfesar ta jawo cece-kuce a kafar sada zumunta ta Twitter a ranar da aka sanar da cewa sarauniyar Ingila na can kwance jina-jina a asibiti.

Kara karanta wannan

Tashin hankali ga 'yan Najeriya yayin da Buhari yace zai haramta amfani da kananzir

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wani rubutu da ta yi a Twitter, ta bayyana cewa, tana fatan sarauniya Elizabeth II ta yi mummunan mutuwa saboda wasu dalilai da ta bayyana.

Wannan magana ta jawo maganganu daga bangarori daban-daban a duniya, ciki har da fitattun 'yan kasuwa irinsu Jeff Bezos; mai kamfanin Amazon.

Bezos ne ya jefa rayuwata cikin matsala

Ta zargi cewa, mai kamfanin na Amazon ya jawo jama'a suna ta yi mata barazana daga bangarori daban-daban na duniya, Pulse ta ruwaito.

Ta bayyana cewa:

“Ina jin kamar rayuwata na cikin hadari. Ba na samun natsuwa da kwanciyar hankali bisa wadannan karairayi da lika min.. Na bar amfani Facebook shekaru hudu da suka gabata."

Ta kuma koka da yadda ake ta'allaka ta da kungiyar nan ta ta'addanci wato IPOB, inda tace sam bata da alaka dasu.

Kara karanta wannan

Za a Gurfanar da Mamu a Gaban Kotu, DSS ta Haramtawa Lauyoyi da 'Yan Uwansa Ganinsa

Ta ce karya ne, kuma babu abinda ya hadata da kungiyar ta 'yan aware.

Twitter Ya Goge Rubutun Wata Farfesar Najeriya da Ta Yiwa Sarauniyar Ingila Fatan Mutuwa Mai Radadi

A tun farko, kamfanin Twitter ya goge wani rubutun farfesa Uju Anya, malama a jami’ar Carnegie Mellon ta Amurka, kan martaninta ga rashin lafiyar Sarauniyar Ingila Elizabeth II.

Twitter ya goge rubutun ne sa'o'i kadan bayan buga shi a ranar Alhamis 8 ga watan Satumba.

A cewar Twitter: "Wannan rubutu ya saba ka'idojin Twitter."

Asali: Legit.ng

Online view pixel