Osinbajo Ya Dira a Landan Gabanin Bikin Jana’izar Sarauniya Elizabeth Ta II

Osinbajo Ya Dira a Landan Gabanin Bikin Jana’izar Sarauniya Elizabeth Ta II

  • Mataimakin shugaban kasa yemi Osinbajo ya shilla birnin Landan a kasar Burtaniya a ranar Asabar 17 ga watan Satumba
  • An samu labarin isarsa, kuma ya je kasar ne domin halartar jana'izar sarauniyar Ingila Elizabeth da ta kwanta dama kwanan nan
  • Osinbajo zai kuma yi amfani da damar wajen halartar wasu taruka masu muhimmanci a Burtaniya

Landan, Burtaniya - Dan Najeriya na biyu, mataimakin shugaban kasan Najeriya, Yemi Osinbajo ya shilla Burtaniya a ranar 17 ga Satumba domin halartar taron sallama da gawar sarauniyar Ingila.

Osinbajo zai wakilci 'yan Najeriya ne da kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari a jana'izar da za a yi na sarauniyar a cikin wannan watan.

Rahoton Vanguard ta bayyana cewa, a yanzu haka Osinbajo na Landan, kuma zai yi amfani da halartar jana'izar wajen shiga wasu taruka da dama a ranakun Asabar da kuma Litinin.

Kara karanta wannan

Mahaifiyar Tsohon Shugaban EFCC, Ibrahim Magu, Ya rasa Mahaifiyarsa

Osinbajo ya dira Landan halartar jana'izar sarauniya Elizabeth
Osinbajo Ya Dira a Landan Gabanin Bikin Jana’izar Sarauniya Elizabeth Ta II | Hoto: akandeoj
Asali: UGC

Hakazalika, zai gana da sakataren wajen Burtaniya, James Cleverly kafin ya dawo Najeriya bayan kammala jana'izar sarauniya a ranar Litinin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Za a binne sarauniya Elizabeth, mai sarauntar da tafi dadewa a duniya za ta a ranar Litinin 19 ga watan Satumba, kamar yadda rahotanni suka sanar.

Osinbajo ya yi ta'aziyya a madadin 'yan Najeriya

Rahoton Channels Tv ya ce, da isar Osinbajo ya sanya sunansa a littafin ta'aziyyar sarauniya kamar yadda al'adar turai ta tanada.

Ya rubuta cewa:

"Najeriya ta shiga sahun gwamnati, jama'ar Burtaniya, kasashen renon Ingila da ma sauran kasashen duniya wajen mika ta'aziyya ga ahalin saraunta game da rashin sarauniya mai dogon zamani. Allah ya albarkaci bayanta."

Hadimin mataimakin shugaban kasan, Laolu Akande ya yada wani rubutu a Twitter don bayyana isar mai gidansa Landan.

Rayuwata Na Cikin Hadari Tun Bayan Yiwa Sarauniyar Ingila Elizabeth II Mummunan Fata, Farfesa Uju Anya

Kara karanta wannan

Osinbajo ya kai ziyara jihar Kano, ya jajantawa sanatan da dansa ya rasu

A wani labarin, Farfesa 'yar Najeriyar nan dake zaune a Amurka da ta yi fatan mutuwa mai radadi ga sarauniyar Ingila ta bayyana cewa, rayuwarta na cikin matsanancin hali.

Uju Anya farfesa ce a sashen Harsunan Zamani a Jami’ar Carnegie Mellon ta kasar Amurka, in ji jaridar The Punch.

Farfesar ta jawo cece-kuce a kafar sada zumunta ta Twitter a ranar da aka sanar da cewa sarauniyar Ingila na can kwance jina-jina a asibiti.

Asali: Legit.ng

Online view pixel