Aika-Aikar Dan China: Gwamnatina Za Ta Dauki Mataki Kan Makashin Ummita, Inji Ganduje

Aika-Aikar Dan China: Gwamnatina Za Ta Dauki Mataki Kan Makashin Ummita, Inji Ganduje

  • Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa za ta tabbatar da doka ta yi aiki kan lamarin kisan Ummita Buhari da ake zargin wani dan China da aikatawa
  • Gwamna Abdullahi Ganduje ya ce dole shari'a ta shigo lamarin domin abu ne da ya shafi zubar da jini
  • A makon jiya ne dai aka wayi gari da labarin kisan matashiyar budurwar bayan mutumin da ake zargi ya kutsa kai gidannsu sannan ya caccaketa da wuka

Kano - Gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ta sha alwashin tabbatar da ganin doka ta yi aikinta a kan lamarin kisan Ummukhulthum Sani Buhari, da ake zargin wani dan kasar China da yi.

Da yake jawabi kan lamarin a gidan gwamnatin jihar, Ganduje ya ce dole maganar shari’a ta shigo ciki kuma sai doka ta yi aikinta tunda har abun ya danganci zubar da jini ne, sashin Hausa na BBC ta rahoto.

Kara karanta wannan

Kungiyar 'yan China a Kano ta yi martani kan kisan da dan China ya yiwa budurwarsa a Kano

Ganduje da Ummita
Aika-Aikar Dan China: Gwamnatina Za Ta Dauki Mataki Kan Makashin Ummita, Inji Ganduje Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Gwamnan ya kuma bayyana cewa tuni suka sa aka tsare wanda ake zargin mai suna Mista Geng Quanrong, bayan jama’a sun kama shi a gidan iyayen marigayiyar a ranar Juma’ar da ta gabata.

A ranar Juma’a, 16 ga watan Satumba ne Mista Geng Quanrong ya kutsa kai cikin gidansu Ummita da ke unguwar Kabuga Janbulo sannan ya caccaketa da wuka.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahoton ya kara da cewa rundunar yan sanda ta jihar Kano ta bayyana cewa tana nan tana ci gaba da gudanar da bincike a kan lamarin.

Kuma tuni ta mika lamarin zuwa ga sashin binciken manyan laifuka a bangaren kisan kai.

Bayan Kisan Ummita, Budurwa ta Fallasa Yadda Take Warwarar Kudin Saurayinta Dan Kasar Waje, Tana Neman Shawara

A wani labarin kuma, mun ji cewa kisan Ummita da wani dan China yayi ya firgita wata budurwa wacce itama tana da saurayi dan kasar waje, a yanzu haka ta rasa sukuni.

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa A 2023: Tinubu Na Da Karfin Da Zai Iya Farfado Da Najeriya, Yahaya Bello

A cikin wani bidiyo da ya yadu a soshiyal midiya, budurwar ta koka cewa ta kasa bacci tun bayan da ta samu labarin kashe Ummita da dan Chinan yayi.

Budurwar wacce ke neman shawarar jama’a, tace ko shakka babu taci kudin mutumin sosai kuma yanzu ta rasa yaya zata yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel