Bayan Kisan Ummita, Budurwa ta Fallasa Yadda Take Warwarar Kudin Saurayinta Dan Kasar Waje, Tana Neman Shawara

Bayan Kisan Ummita, Budurwa ta Fallasa Yadda Take Warwarar Kudin Saurayinta Dan Kasar Waje, Tana Neman Shawara

  • Wata matashiyar budurwa da ba a bayyana sunanta ba ta shiga tashin hankali bayan samun labarin kisan da dan China ya yiwa Ummita
  • Budurwar ta damu ne domin itama tana da saurayi dan kasar waje wanda taci kudinsa ba kadan ba
  • A cikin wani bidiyo, an gano budurwar tana rokon jama'a da su tayata da addu'a tare da bata shawarwari kan abun da yakamata tayi a yanzu

A makon jiya ne wani dan kasar China ya je har cikin gida ya halaka budurwarsa ‘yar Kano mai suna Ummita a unguwar Janbulo da ke jihar Kano.

Wannan al’amari ya firgita wata budurwa wacce itama tana da saurayi dan kasar waje, a yanzu haka ta rasa sukuni.

A cikin wani bidiyo da ya yadu a soshiyal midiya, budurwar ta koka cewa ta kasa bacci tun bayan da ta samu labarin kashe Ummita da dan Chinan yayi.

Kara karanta wannan

Kungiyar 'yan China a Kano ta yi martani kan kisan da dan China ya yiwa budurwarsa a Kano

Budurwa
Bayan Kisan Ummita, Budurwa ta Fallasa Yadda Take Warwarar Kudin Saurayinta Dan Kasar Waje, Tana Neman Shawara Hoto: garkuwanarewa_.
Asali: Instagram

Budurwar wacce ke neman shawarar jama’a, tace ko shakka babu taci kudin mutumin sosai kuma yanzu ta rasa yaya zata yi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta ce:

“Jama’a, bacci nake so nayi na kasa. Hmmm wani abu ne yake bala’in damuna, dan Allah ku bani shawara. Soyayya nake yi da wani dan kasar waje, bana so in fadi kasar, kuma har ga Allah naci kudinshi, naci kudinshi, naci kudinshi. Abun da ya faru da Ummita ya tsaya mun a rai, yanzu ni yaya zanyi? Ku bani shawara.
“Na shiga uku, innalillahi wa’inna illaihi raji’un, dan Allah kada ku dauki abun nan wasa, jama’a ku bani shawara.”

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

fulata_mahre ya ce:

"Naakulle da makulli kaff ."

bin_saleehu ya yi martani:

"Ko kudinsa ko aurensa tunda ba damu kika ci kudinba mayaudariyya."

Kara karanta wannan

Yadda saurayin diyata dan China ya shiga har gida ya caccaka mata wuka, inji mahaifiyar Ummita

itx_reality ya ce:

"Kunfi kusa ."

mairodahiru20 ta ce:

"Gani ga wane dai."

b______________black ya ce:

"Too ki aure shi mana ko ki biya shi kudin sa ko ki yarda yayi abunda zai dake na kudin sa ‍♂️Tunda ku mayun kudi ne."

ramlah_collection_7886 ta ce:

"In kina sonshi ki aure Shi in ya yarda zai karbi muslinci ko ki nemeshi kibashi kudinshi kuyi sulhu"

Zan Saketa Bayan Wata 2 Sai Muyi Aurenmu: Matashi Ya Sanar Da Budurwarsa Labarin Aurensa Da Wata Daban

A wani labarin, wata matashiyar budurwa ta shiga halin damuwa bayan samun labarin auren saurayinta da suke soyayya da juna.

A wata wallafa da tayi a shafinta na Twitter, budurwar mai suna Salma ta bayyana yadda saurayin da take matukar kauna ya sanar da ita batun aurensa da wata daban.

Ko da ya sanar da Salma cewa ya yi aure da fari bata yadda ba don duk a zatonta zolayarta yake yi.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Hirar Karshe Da Budurwar Da Dan China Ya Kashe Tayi Da Kawarta, Ya Kasance Akan Mutuwa

Asali: Legit.ng

Online view pixel