Shugaban Kasa A 2023: Tinubu Na Da Karfin Da Zai Iya Farfado Da Najeriya, Yahaya Bello

Shugaban Kasa A 2023: Tinubu Na Da Karfin Da Zai Iya Farfado Da Najeriya, Yahaya Bello

  • Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya nuna yakinin cewa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu zai iya dawo da martabar Najeriya idan ya dare kujerar Buhari a 2023
  • Bello ya ce Tinubu yana da alkibla da tsarin shugabanci irin wanda Najeriya ke bukata don magance matsalolinta
  • Gwamnan ya ba da tabbacin cewa jihar Kogi ta Tinubu ce da duk wasu yan takarar APCda ke neman mukamai a zabe mai zuwa

Kogi - Gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello ya nuna karfin gwiwa cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressive Congress (APC), Sanata Bola Ahmed Tinubu, zai iya dawo da Najeriya kan tafarkin ci gaba idan ya dare kujerar shugabanci.

Gwamna Bello, wanda ya ce kungiyar yakin neman zaben BAT ta nada shi a matsayin jagoran matasa na kasa, ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi, yayin ganawa da yan takarar kujerun ciyamomi da sauran masu ruwa da tsaki daga mazabar Idah ta jihar.

Kara karanta wannan

Duk Karya Ce, APC Tayi Watsi Da Zaben Yanar Gizo Na Cewa Peter Obi Yafi Samun Karbuwa

Tinubu da Bello
Shugaban Kasa A 2023: Tinubu Na Da Karfin Da Zai Iya Farfado Da Najeriya, Yahaya Bello Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Ya bayyana cewa Tinubu yana bin tsarin jam’iyyar a kullun, ya nuna alkibla da shugabanci irin wanda kasar ke bukata don magance matsalolinta don haka dole a bashi goyon baya tare da zabarsa a 2023.

Gwamnan ya kuma ce jihar Kogi ta Tinubu ce kawai kuma za ta yi aiki don tabbatar da ganin cewa dan takarar da sauran zababbun yan takarar APC sun yi nasara, Nigerian Tribune ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma jadadda cewa mabiya jam’iyyar da shugabanni sune dakaru a lokacin zabe don haka akwai bukatar a tafi da kowa a matsayin tsintsiya madaurinki daya kuma amfanin zai zo kai tsaye ga masu yiwa jam’iyya biyayya sabanin yadda ake yi a baya.

Ya ce an yi zantawar ne don sake ba mutanen mazabar tabbacin hadin kan jam’iyyar, yana mai umurtansu da kada su shiga harkokin da suka saba jam’iyya, jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Mance Da Batun Tinubu, Ya Fadi Wanda Zai Sa Ya Gaji Buhari Da Yana Da Iko

2023: Tinubu Ya Naɗa Gwamna Bello Matsayin Shugaban Yakin Neman Zabe Na Matasa

A gefe guda, mun ji cewa an naɗa gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, a matsayin shugaban matasan tawagar yakin neman zaɓen Tinubu-Shettima a jam'iyyar APC.

Vanguard ta ruwaito cewa wannan naɗin na cikin wata takarda mai adireshin Yahaya Bello ɗauke da sa hannun ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

A takardar Tinubu ya jaddada cewa gwamna Bello na ɗaya daga cikin manema tikitin takara a zaɓen fidda gwanin APC ta suka cancanci wannan babban matsayi duba da nasarorinsa a matsayin gwamna da mamban jam'iyya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel