Ina Mai Rokonka Dan Allah, Ka Kula Da Diyata: Uba Ya Fashe Da Kuka Yayin Da Ya Roki Surukinsa A Bidiyo

Ina Mai Rokonka Dan Allah, Ka Kula Da Diyata: Uba Ya Fashe Da Kuka Yayin Da Ya Roki Surukinsa A Bidiyo

  • Wani bidiyon bikin aure da ya yadu ya nuno lokacin da wani dan Najeriya ya roki surukinsa da ya kula masa da diyarsa da kyau
  • Ya kai har sai da mutumin ya fashe da kuka yayin da yake jawabinsa a bidiyon bikin wanda tuni ya yadu
  • Bidiyon mai tsuma zuciya ya haifar da martani daga yan Najeriya a shafukan soshiyal midiya inda da yawansu suka taya mutumin roko

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Wani bidiyon shagalin biki da ya yadu a soshiyal midiya, ya nuno yadda wani uba dan Najeriya ya fashe da kuka yayin da yake jawabi a ranar auren diyarsa.

An jiyo dattijon da ke magana a harshen Yarbanci yana rokon surukin nasa a kan ya yiwa Allah ya kula masa da diyarsa.

Da yake ci gaba da rokon mijin diyar tasa, sai mutumin ya fashe da kuka har sai da amaryar wacce ke tsaye a gefenshi ta rungume shi da sigar rarrashi.

Kara karanta wannan

Abun Ba Sauki: Matashiyar Baturiya Da Aka Gano Tana Tallan Gyada Ta Magantu A Sabon Bidiyo

Uba da diyarsa
Ina Mai Rokonka Dan Allah, Ka Kula Da Diyata: Uba Ya Fashe Da Kuka Yayin Da Ya Roki Surukinsa A Bidiyo Hoto: @instablog9ja.
Asali: Instagram

Masu amfani da soshiyal midiya sun yarda cewa a kan samu irin wannan yanayi mai tsuma zuciya a duk lokacin da uba zai aurar da diyarsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@mr_hyenana ya ce:

“Wannan ba rauni bane.”

@cutefayy ta ce:

“Kada ka illata masa diyarsa.”

@amaxynaturals ta ce:

"Awwwww. Wannan abu akwai tsuma rai. Kada ka damu Dadi zai kula maka da ita da izinin Allah.”

@magamudi ta ce:

“Soyayyar uba. Babu kamarsa.”

Saurayi Da Budurwa da Suka Fara Soyayya A Makarantar Firamare Sun Yi Aure, Hotunan Bikinsu Ya Yadu

A wani labarin, mun ji cewa yayin da wasu ke shafe tsawon rayuwarsu wajen neman masoyi na gaskiya, wani saurayi da budurwarsa da suka hadu a makarantar firamare sun shiga daga ciki a wani kayataccen biki.

Kara karanta wannan

Bidiyon Mutumin da Ya Shiga Jirgin Sama, Ya Bai wa Kowanne Fasinja N42k Ya Dauka Hankali

Brianna Ragbeer da Romane Cameron sun shiga babbar makaranta tare inda suka zama masoyan usuli a makarantar sakandare.

Brianna ta tuna fitarsu ta farko a matsayin masoya, suna je wani gidan kallo inda suka fallasa wa junansu asirin zukatansu da kuma kallon fim a tare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel