Bidiyon Mutumin da Ya Shiga Jirgin Sama, Ya Bai wa Kowanne Fasinja N42k Ya Dauka Hankali

Bidiyon Mutumin da Ya Shiga Jirgin Sama, Ya Bai wa Kowanne Fasinja N42k Ya Dauka Hankali

  • Bidiyon wani mutumi yana rabawa jama'a kudi a cikin jirgin sama ana tsaka da tafiya a sararin saminya ya janyo cece-kuce a soshiyal midiya
  • A gajeren bidiyon , an ga mutumin yana mika kudin ga fasinjojin yayin da suka dinga kuranta shi domin nuna godiya
  • Bidiyon mai birgewa ya yadu a Instagram inda ya janyo martani daban-daban daga jama'ar da suka kalle shi

Wani mutumi mai karamci kuma mai kumbar susa ya bayyana a wani bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumuntar zamani inda yake bai wa fasinjojin jirgin sama kyautar N42,000 kowanne.

A gajeren bidiyon, an ga mutumin ya shiga jirgin saman da salon biloniyoyi inda yake rarraba kudaden sabbi dal.

Miloniya
Bidiyon Mutumin da Ya Shiga Jirgin Sama, Ya Bai wa Kowanne Fasinja N42k Ya Dauka Hankali. Hoto daga @bcrworldwide
Asali: UGC

Kowanne fasinja ya samu yawan kudi daya

Bidiyon an gano an nade shi ne a jirgin da ya tashin zuwa Las Vegas dake Amurka amma 'yan Najeriya da suka ga bidiyon sun bayyana cewa ya birgesu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wasu daga cikin tambaya suke idan mutumin zai taba zuwa Najeriya yayi irin hakan.

Kalla Bidiyon:

'Yan Soshiyal Midiya sun yi martani

@ardnas_ego:

"Dama biloniya yayi wannan abun a jirgin kamfanin Airpeace yayin da nake ciki."

@meet_mimi_ :

"Ina jirgin yake yanzu? Ina iya zama a wani wurin in jira su sannan in karba nawa kason. Allah ya karawa mai bayarwa arziki."

@orissabel3788:

"Ba wai fata kawai ba fa... Idan kai biloniya ne zaka bayar?"

@fumceejaycee_hair:

"Ubangiji ka sanya min albarkarka yadda zan dinga bayarwa. Babu abinda ya kai bayarwa dadi amma mutane da yawa basu san hakan ba."

@chimankpamosondu:

"Bayarwa a kullum tana da dadi... Ina fatan albarkar Ubangiji."

@oneheart_but_two:

"Wannan dai ba zai taba zuwa Najeriya ya shiga Airpeace ba ko, a take zan bayyana nima."

@arthurdsage:

"Zaka iya farawa da 'yan dubban da kake da su, ba sai ka jira har ka zama biloniya ba."

Jarabar Mijina ta Ishe ni, Neman Hakkinsa Yake da Azumi ko Ina Al'ada, Matar Aure ga Kotu

A wani labari na daban, wata matar aure mai suna Zainab Yunusa ta bukaci kotun shari'a dake zama a Magajin Gari, Kaduna, ta ta tsinke igiyar aurenta da mijinta mai suna Alhaji Ali garba Ali saboda tsabar jarabarsa.

Daily Trust ta rahoto, mai karar a ranar laraba ta sanar da kotu cewa Garba na neman jima'i ko a lokutan da take al'adan da lokacin azumin watan Ramadan.

Zainab tace sun yi zaman aure na shekara daya kacal inda ta kara da cewa ta bar gidansa ne saboda wannan lamarin.

Wacce ke karar ta yi bayanin cewa a yayin zamansu, Garba ya saba dawowa gida har da rana a lokutan da take jinin al'ada don ya kwanta da ita, wanda addinin Islama bai aminta da hakan ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel