Saurayi Da Budurwa da Suka Fara Soyayya A Makarantar Firamare Sun Yi Aure, Hotunan Bikinsu Ya Yadu

Saurayi Da Budurwa da Suka Fara Soyayya A Makarantar Firamare Sun Yi Aure, Hotunan Bikinsu Ya Yadu

  • Wasu masoya da suka hadu a makarantar firamare sun shiga daga ciki a wani biki mai matukar birgewa
  • Brianna Ragbeer da Romane Cameron sun shiga babbar makaranta tare inda suka ci gaba da soyewarsu
  • An daura auren masoyan a ranar 6 ga watan Agusta a wani bikin sirri da a Portmore, St Catherine a Jamaica

Jamaica - Yayin da wasu ke shafe tsawon rayuwarsu wajen neman masoyi na gaskiya, wani saurayi da budurwarsa da suka hadu a makarantar firamare sun shiga daga ciki a wani kayataccen biki.

Brianna Ragbeer da Romane Cameron sun shiga babbar makaranta tare inda suka zama masoyan usuli a makarantar sakandare.

Amarya da ango
Masoyan Da Suka Hadu A Makarantar Firamare Sun Yi Aure, Hotunan Bikinsu Ya Yadu Hoto: @JamaicaGleaner
Asali: Twitter

Brianna ta tuna fitarsu ta farko a matsayin masoya, suna je wani gidan kallo inda suka fallasa wa junansu asirin zukatansu da kuma kallon fim a tare.

Kara karanta wannan

Mayakan Boko Haram Sun Kashe Babban Limami Da Wasu Mutum 3 A Jihar Borno

Tun daga wannan lokacin, masoyan sun mayar da wajen kallo dandalin farkado da soyayyar da suke yiwa junansu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ko bayan da Brianna ta koma Amurka da zama hakan bai kawo tangarda a soyayyarsu ba. Kowannensu baya son rabuwa da dan uwansa, sun ci gaba da soyayyarsu a yanar gizo tsawon shekaru biyu.

Bayan sun shafe tsawon shekaru bakwai tare, Romane ya nemi burin ransa ta zama matarsa.

“Na durkusa kan guiwana daya sannan na tambayeta, za ki aure ni? Sannan ta amsa da eh,” cewar Romane kamar yadda kafar sadarwar The Cleaner ta rahoto.

Amaryar ta shirya aurenta da taimakon yan uwa da abokai, kuma a ranar 6 ga watan Agusta, Brianna da Romane suka zama mata da miji a wani biki da aka yi cikin sirri a Portmore, St Catherine.

Kara karanta wannan

Ruwa Yayi Awon Gaba da Sama da 'Yan Boko Haram 70 Sakamakon Luguden Sojojin Najeriya

Kalli hotunansu a nan.

Tsoffin Maza Sun Fi Iya Soyayya: Matashiya Yar Shekaru 30 Da Ta Auri Dan Shekaru 80

A wani labarin, wata mata da ta dulmiya a cikin soyayya ta baiwa mutane da dama mamaki bayan ta bayyana irin soyayyar da suke sha da sahibinta, wanda zai iya yin kaka da ita.

Matashiyar wacce ta fito da Mudaka, yankin Kudancin Kivu a damokradiyyar Kongo, ta ce soyayya babu ruwansa da banbancin shekaru kuma bai da iyaka.

Tsawon shekaru biyu kenan da Mwamini ta auri burin ranta Katembela Etienne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel