Abun Ba Sauki: Matashiyar Baturiya Da Aka Gano Tana Tallan Gyada Ta Magantu A Sabon Bidiyo

Abun Ba Sauki: Matashiyar Baturiya Da Aka Gano Tana Tallan Gyada Ta Magantu A Sabon Bidiyo

  • Baturiyar da ta baiwa mutane mamaki bayan an gano ta a titin Lagas tana tallan gyara ta fito ta bayyana abubuwan da ta fuskanta a wannan rana
  • Ta ce ta ji dadin yanayin amma dai gaskiya mutanen da ke yawo da kaya a kansu da sunan talla suna shan wahala
  • Sabon bidiyon ya kayatar da yan Najeriya da dama inda suka jinjina mata kan kwaikwayon al’adar kasar duk da kasancewarta baturiya

Lagas - Bayan ta karade titin Lagas tana tallan gyada, matashiyar baturiya mai suna Pia, ta siye zukatan yan Najeriya da dama.

Ta wallafa sabon bidiyo inda take bayanin yadda harkoki suka gudana a wannan rana da kuma dalilinta na aikata abun da ta yi.

Kara karanta wannan

Matashiyar Budurwar Najeriya Ta Wanke Kafa Har Turai Don Ganawa Da Baturen Da Ta Hadu Da Shi A Yanar Gizo

Baturiya
“Abun Ba Sauki Ko Kadan”: Matashiyar Baturiya Ta Jinjinawa Yan Talla Bayan Ta Yi Tallan Gyada Hoto: TikTok/@majiq.pia.
Asali: UGC

A cewar Pia, ta so yin hulda da mutane ne da kuma jin abun da ake ji a cikin talla a karkashin rana.

Ta kuma tabbatar da wahalar da ke cikin yin irin wannan sana’a yayin da ta jinjinawa masu yin ta. Ta burge yan Najeriya da dama inda suka yaba kyawawan halayyenta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kalli bidiyon a kasa:

Jama’a sun yi martani

@Kuzari ya ce:

“Na gan ki a wannan rana lokacin ina a cikin motata kuma sai naji kamar na rungume ki.”

@Abel ta yi martani:

“Ke din ta dabance! Mijinkin ya yi dace. Marabanki da zuwa Najeriya. Muna kaunarki.”

@_Anne_O ta ce:

“Kina jin dadin rayuwa a Najeriya tare da rungumar duk abun da zai faranta lokacinki a can da kuma nuna kyawunsa.”

@Jane ta ce:

“Mungode yar’uwa yanzu na rada maki suna Naanzem a hukumance. Kin fara zama yar Najeriya. Ki ci gaba.”

Kara karanta wannan

Yadda Hannu a Karbar Kudin Fansa har N2b da Alaka da Kungiyar Ta'addanci ta sa aka Kama Mamu

Neman Na Goro: Bidiyon Kyakkyawar Baturiya Tana Tallan Gyada A Titin Lagas Ya Yadu

A baya mun kawo cewa jama’a sun yi cece-kuce kan bidiyon wata kyakkyawar baturiya tana tallan gyara a tsakiyan titin Lagas inda aka samu cunkoson ababen hawa.

Baturiyar ta sanya atampa dinkin doguwar riga da faranti daure a kanta yayin da take tallata haajarta ga matafiya da direbobi.

Wani bangare na bidiyon ya nunota tana zantawa da wani direba wanda ke son siyan haajarta. Direban ya tambayi kudaden gyadar, inda ta amsa cewa N500 ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel