Zulum Ya Ziyarci Iyalan Kwamandan CJTF Da Boko Haram Suka Kashe, Ya Yi Musu Babban Alheri

Zulum Ya Ziyarci Iyalan Kwamandan CJTF Da Boko Haram Suka Kashe, Ya Yi Musu Babban Alheri

  • Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum ya ziyarci iyalan marigayi Babagana Tela (Kadau), tsohon kwamandan CJTF na Bama da Boko Haram suka kashe
  • Bayan musu ta'aziyya bisa rasuwar Kadau, Zulum ya basu kyautan N10m da kuma wani umurtar a siya musu gida na N10m tare da daukan nauyin karatun yaran da mamacin ya bari
  • Zulum ya ce wannan karamcin ba wani abu bane idan aka kwatanta da gudunmawar da Kadau ya bada wurin samar da zaman lafiya a Bama da Borno baki daya

Borno - Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno ya bada kyautan gida da Naira miliyan 10 ga iyalan tsohon kwamandan yan sa kai na civilian JTF, Babagana Tela, wanda Boko Haram suka kashe.

Mista Tela wanda aka fi sani da 'Kadau' saboda jarumtarsa shine kwamandan JTF a Bama, daya daga cikin garuruwan da aka kwato a Borno, Daily Nigerian ta rahoto.

Kara karanta wannan

Kwanaki 9 Da Bada Umurnin Damke Ado Gwanja, Safarau Da Yan TikTok 8, Har Yau Ba'a Kamasu Ba

Zulum visits Kadau Family
Zulum Ya Ziyarci Iyalan Kwamandan CJTF Da Boko Haram Suka Kashe, Ya Yi Musu Babban Alheri. Hoto: Borno Governor
Asali: Facebook

Ya rasu ne a harin kwantar bauna da yan ta'addan suka yi a watan Yuni.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yan sa kai din suna amfani da ilimin su na sanin lunguna da sakuna a Borno don taimakawa sojoji yakar yan ta'addan.

Sanarwar da Isa Gusau, mashawarcin Gwamna Zulum a bangaren watsa labarai ya fitar ta ce gwamnan wanda ya ziyarci iyalan mamacin ya kuma amince gwamnati ta dauki nauyin karatun yaransa.

Wani bangare na cikin sanarwar ta ce:

"Gwamna ya bada umurnin a bada N10m don kula da iyalan mamacin na wani lokaci, ya bukaci su bude asusun baki na hadin gwiwa inda za a saka kudin.
"Zulum ya kuma umurci a fitar da Naira miliyan 10 a siya wa iyalan Kadau gida saboda su dena biyan kudin haya.
"Zulum ya kara da cewa gwamnatin jiha za ta dauki nauyin karatun yayan marigayin har su kammala.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Gini Mai Hawa 4 Ya Rushe Ya Fada Kan Mutane Da Dama A Ibadan

"Gwamnan ya ce bayyana karamcin da aka musu a matsayin karamin tukwici idan aka kwatanta da gudunmawar da ya bada wurin dawo da zaman lafiya a Bama da Borno da Najeriya baki daya."

Ya kara da cewa gwamnan ya kuma bada kudi da kayan abinci da tufafi fa sauran yan sa kai guda 683 a yankin.

Borno: Zulum Ya Biya Naira Miliyan 5 Don Daukan Nauyin Karatun Wani Hazikin Yaro Mai Shekara 13 a Maiduguri

A wani rahoton, Zulum ya bada Naira miliyan 5 ga wata makaranta mai zaman kanta domin daukan nauyin karatun Musa Sani, yaro dan shekara 13 mai hazaka a Borno wanda ya yi amfani da laka ya kwaikwayi ginin gadan sama ta farko a jihar da ke custom round about a Maiduguri.

An biya kudin ne ga hukumar makarantar Golden Olive Academy, Maiduguri, domin daukan nauyin karatun Musa daga ajin frimare na hudu har kammala babban sakandare, Nigerian Tribune ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel