Borno: Zulum Ya Biya Naira Miliyan 5 Don Daukan Nauyin Karatun Wani Hazikin Yaro Mai Shekara 13 a Maiduguri

Borno: Zulum Ya Biya Naira Miliyan 5 Don Daukan Nauyin Karatun Wani Hazikin Yaro Mai Shekara 13 a Maiduguri

  • Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum ya biya naira miliyan 5 a matsayin tallafin wani hazikin yaro a Maiduguri
  • Yaron, Musa Sani, mai shekaru 13 ya yi amfani da laka ne ya kwaikwayi gadar sama ta farko da aka gina a Maiduguri wacce Shugaba Buhari ya kaddamar
  • Wannan nuna basirar ce ta bawa Zulum sha'awa ya gana da iyayen yaron da ke aji 3 na frimare ya kuma biya masa kudin makaranta har ya kammala babban sakandare a wata makaranta mai zaman kanta don karfafa masa gwiwa

Borno - Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno ya bada Naira miliyan 5 ga wata makaranta mai zaman kanta domin daukan nauyin karatun Musa Sani, yaro dan shekara 13 mai hazaka a Borno wanda ya yi amfani da laka ya kwaikwayi ginin gadan sama ta farko a jihar da ke custom round about a Maiduguri.

Kara karanta wannan

Bidiyon mai digirin digir yana tallar kwai a titi, ya nemi aiki sau 5000 bai samu ba

Musa Sani.
Zulum Ya Biya Naira Miliyan 5 Don Daukan Nauyin Karatun Wani Hazikin Yaro Mai Shekara 13 a Borno. @nigeriantribune.
Asali: Twitter

An biya kudin ne ga hukumar makarantar Golden Olive Academy, Maiduguri, domin daukan nauyin karatun Musa daga ajin frimare na hudu har kammala babban sakandare, Nigerian Tribune ta rahoto.

Iyayen Musa, dan ajin frimare na 3 Community School da ke Gwange a Maiduguri, ba masu hannu da shuni bane.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin yan kwanakin nan ne hankalin Zulum ta kai ga Musa bayan ya yi amfani da laka ya gina kwafin gadar sama da Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar a watan Disamba a Maiduguri.

Zulum ya yi sha'awar basirar da yaron ke da shi hakan yasa gwamnan ya nemi ganin iyayensa kuma ya bada tallafin karatun don a inganta basirarsa.

Hukumar ETF ta biya N5,029,000 ga makaranar da Musa zai cigaba da karatu

Kamar yadda gwamnan ya bada umurni, Hukumar Asusun Tallafin Ilimi na Jihar Borno, (ETF) za ta dauki nauyin karatun yaron, shugaban ETF, Farfesa Hauwa Biu, ta gabatar da chek din miliyan biyar da dubu ashirin da tara (N5,029,000) tare da biyan kudin ga makaranta mai zaman kanta da Musa ya ke karatu a yanzu.

Kara karanta wannan

Ci gaba: Dangote ya sake banke mutum 20, ya zama na 63 a jerin masu kudin duniya

Farfesa Biu ta gode wa Zulum bisa tallafin ta kuma bukaci yaron ya mayar da hankali kan karatunsa domin gwamnan ya yi alfahari da shi nan gaba.

Kaduna: El-Rufa'i' Ya Bada Umurnin A Ɗauki Sabbin Malamai 10,000 Bayan Ya Kori 2,000

A wani rahoton, Gwamna Nasir El-Rufa'i na Jihar Kaduna ya bawa hukumar Ilimi bai ɗaya na Jihar Kaduna, KADSUBEB, ta dauki sabbin malamai 10,000.

Tijjani Abdullahi, shugaban KADSUBEB ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwar a ranar Juma'a, The Cable ta rahoto.

Abdullahi ya ce za a bude shafin daukan malaman na tsawon makonni biyu daga 21 ga watan Yulin, 2022, ya kara da cewa Jami'ar Jihar Kaduna, KASU, ce zata tsara shafin na intanet.

Asali: Legit.ng

Online view pixel