Kwanaki 9 Da Bada Umurnin Damke Ado Gwanja, Safarau Da Yan TikTok 8, Har Yau Ba'a Kamasu Ba

Kwanaki 9 Da Bada Umurnin Damke Ado Gwanja, Safarau Da Yan TikTok 8, Har Yau Ba'a Kamasu Ba

  • Kotun Shari'a ta bukaci kwamishanan yan sandan Kano ya damke Ado Gwanja da wasu mutum 9
  • Kwanaki tara da bada wannan umurni, har yanzu hukumar yan sanda bata kama mutum ko guda cikinsu ba
  • Ana zargin mawaki Ado Gwanja da yin wakokin rashin kunya da tayar da sha'awa cikin matasa

Wata kotun shari'a ta umurci hukumar yan sanda ta damke wasu mutum 10 kuma ta bincikesu kan koyawa matasa rashin tarbiyya a kafafen ra'ayi da sada zumunta, wani jami'in kotun ya bayyanawa AFP ranar Alhamis.

Kotun ta bada umurnin ne tun ranar Talatar makon jiya bayan lauyoyi sun shigar da kara inda suka bukaci hukunta Ado Gwanja da ire-irensa bisa wakokin rashin tarbiyya da daurawa a yanar gizo, jami'in kotun Baba-Jibo Ibrahim ya bayyana hakan.

A rahoton ChannelsTV, wadanda ake zargi maza hudu da mata shida sun hada da mawaki Ado Gwanja, wata 'yar fim da yan Tik-Tok 8.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Gini Mai Hawa 4 Ya Rushe Ya Fada Kan Mutane Da Dama A Ibadan

Ado Gwanja
Kwanaki 9 Da Bada Umurnin Damke Ado Gwanja, Safarau Da Yan TikTok 8, Har Yau Ba'a Kamasu Ba
Asali: Facebook

A cewar Baba-Jibo:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Kotun Shari'ar ta bada umurni ga kwamishanan yan sanda ya damke wadannan mutum 10 kuma a gudanar da bincike kan rawar da suka taka wajen bayyanawa rashin tarbiyya."

Ana zargin Ado Gwanja da sakin waka mai suna "A Sosa".

Amma kwanaki tara bayan da kotu ta bada wannan umurnin, har yanzu ba'a damkesu ba, Ibrahim yace.

A cewarsa:

"Zamu jira kammaluwar binciken da yan sanda ke yi domin sanin matakin da kotu zata dauka."

Gwamnatin Buhari Ta Hana Gidajen Rediyo Sanya Wakar ‘Warr’ da 'A Sosa' Na Ado Gwanjo

Makwannin da suka gabata ne kafafen sada zumunta a Arewacin Najeriya suka dauki dumi yayin da wani mawakin Hausa, Ado Gwanja ya saki wata waka mai cike da maganganun da suka saba al'ada.

Malamai da masu tsokaci sun yi ca kan wakokin 'Warr' da 'A Sosa', inda suka zargi Gwanjo da kawo wani sabon salon bata tarbiyya da kawo tsaiko ga al'adar Mallam Bahaushe.

Kara karanta wannan

Allah-wadai: Rikici ya barke tsakanin Mali da Cote D'Ivoire, Buhari ya sha alwashin warwarewa

Bayan cece-kuce da koke daga malamai da masu sharhin lamurran yau da kullum, gwamnati ta bayyana daukar mataki kan gidajen rediyo dake yada wakar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel