Gini Mai Hawa 4 Ya Rushe Ya Fada Kan Mutane Da Dama A Ibadan

Gini Mai Hawa 4 Ya Rushe Ya Fada Kan Mutane Da Dama A Ibadan

  • Kimanin bakwai ne suka samu munanan rauni sakamakon wani gini da ya rufta a Awosika, karamar hukumar Ibadan ta Arewa, Jihar Ibadan
  • Rahotanni sun bayyana cewa gini mai hawa hudu ya rufta ne misalin karfe 5.45 na safiyar ranar Alhamis 8 ga watan Satumba
  • Jami'an hukumar kwana-kwana, jami'an hukumar kiyayye hadura na kasa, FRSC sun yi nasarar ceto mutum bakwai

Ibadan - A kalla mutane bakwai ne suka jikkata bayan wani gini da ba a kammala ba mai hawa biyar ya rufta a safiyar ranar Alhamis, rahoton Nigerian Tribune.

Ginin da ya ruftan yana kusa da wasu sabbin bankunan zamani a Awosika da ke karamar hukumar Ibadan ta Arewa a Jihar Oyo.

Gini Ya Rushe
Gini Mai Hawa 5 Ya Rufta Kan Mutane A Ibadan. Hoto: Nigerian Tribune.
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Sake Buɗe Wa Jami'an 'Yan Sanda Wuta, Rayuka Sun Salwanta

Tawagar masu ceto tare da mutanen unguwar da wadanda ke wucewa sun yi nasarar ceto mutane bakwai kuma a yanzu ana musu magani a asibitin koyarwa na Jami'ar Ibadan.

Wani wanda abin ya faru a idonsa ya bayyana cewa lamarin ya faru ne misalin karfe 5.45 na asubahi a lokacin da musulmi suke dawowa daga sallar asubahi.

Kazalika, tawagar masu kawo dauki da ta kunshi jami'an kwana-kwana, jami'ar hukumar kiyayye hadura, FRSC da wasu jami'an tsaro sun dira wurin domin tallafawa wanda abin ya shafa.

A halin yanzu da aka hada wannan rahoton, babu labarin cewa wani ya rasa ransa saboda afkuwar lamarin baya ga wadanda suka yi munanan rauni.

Ga bidiyon ginin da ya rufta a nan kasa:

Kano: Yara 3 Sun Mutu Yayin Da Dakin Mahaifiyarsu Ya Rushe Ya Rufta Musu

A wani rahoton, wani abin bakin ciki ya faru a kauyen Tarai na karamar hukumar Kibiya a Kano bayan rushewar wani gini da ya yi sanadin rasuwar yara uku yan gida daya.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Jami'an DSS Sun Kai Samame Gidan Tukur Mamu, Sun Kwashe Kwamfuyutoci da Takardu

Mahaifin wadanda suka rasu, Abubakar Usman ya shaidawa babban sakataren SEMA, Saleh Jili lokacin da ya jagoranci wata tawaga zuwa ta'aziyya a garin.

Ya ce wadanda suka rasu suna Umar Abubakar, Aliyu Abubakar da yar uwarsu Aisha Abubakar, kamar yadda The Punch ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel