Hotunan Ummi, Kyakkyawar Budurwar Da Ta Rasa Ranta A Farmakin Da Yan Bindiga Suka Kai Bankunan Kogi

Hotunan Ummi, Kyakkyawar Budurwar Da Ta Rasa Ranta A Farmakin Da Yan Bindiga Suka Kai Bankunan Kogi

  • Wata kyakkyawar budurwa mai suna Ummi ta gamu da ajalinta a yayin harin da yan fashi da makami suka kai bankuna a jihar Kogi
  • Marigayiya Ummi na tsaye kusa da daya daga cikin bankuna uku da aka farmaka lokacin da harbin bindiga ya zo ya same ta, nan take rai yayi halinsa
  • A ranar Talata ne wasu yan bindiga suka farmaki rassan bankuna uku, UBA, Zenith da kuma First Bank a yankin Ankpa, jihar Kogi, inda suka kwashi kuɗi iya son ransu

Kogi - Wata matashiyar budurwa mai suna Ummi ta rasa ranta a yayin farmakin da yan bindiga suka kai garin Ankpa, karamar hukumar Ankpa ta jihar Kogi a ranar Talata, 6 ga wata Satumba.

Wani da lamarin ya faru a idonsa ya ce harbin bindiga ne ya kashe matashiyar budurwar wacce ke kusa da daya daga cikin bankunan da aka yiwa fashin a wannan lokacin, shafin LIB ya rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Najeriya Ba Za Ta Zauna Lafiya Ba Idan Mulki Ya Tsaya A Arewa, In Ji PANDEF

Matashiyar budurwa da aka kashe
Hotunan Ummi, Kyakkyawar Budurwar Da Ta Rasa Ranta A Farmakin Da Yan Bindiga Suka Kai Bankunan Kogi Hoto: LIB
Asali: UGC

An tattaro cewa kimanin makonni biyu da suka gabata ne marigayiyar ta kammala karatunta daga kwalejin Kimiyya ta Glory Land da ke Ankpa.

An rahoto cewa yan fashi da makamin fiye da 15 sun farmaki bankuna uku da misalin karfe 3:00 na ranar Talata, sannan suka yiwa bankunan da kwastamomi fashi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata da ta san marigayiya Ummi mai suna Zuliahat Gold ta je shafinta na Facebook don nuna alhinin wannan rashi tare da wallafa hotunan marigayiyar.

Rundunar yan sandan jihar Kogi ta tabbatar da harin

A halin da ake ciki, kakakin yan sandan jihar, SP William Ayah, ya tabbatar da faruwar lamarin a wani jawabin manema labarai a ranar Laraba, 7 ga watan Satumba.

A cewarsa, yan fashi da makamin sun farmaki bankuna uku a lokaci guda a garin Ankpa, Nigerian Tribune ta rahoto.

Kara karanta wannan

Wani Matashi Ya Koma Jami'ar Da Yayi Karatu, Yace Su Bashi Kudinsa Su Karbi Kwalinsu

Ya kuma ce kwamishinan yan sandan jihar, CP Edward Egbuka, ya jagoranci wata tawaga zuwa wajen faruwar lamarin don ganin irin barnar da maharan suka yi sannan ya yi umurnin karo jami’an tsaro don dawo da zaman lafiya a yankin.

CP Egbuka ya kuma umurci mataimakin kwamishinan yan sanda da ke kula da sashin bincike na SCID da ya fara bincike don gano musababbin harin, tare da bin sahun yan bindigar don gurfanar da su.

Ya kuma bukaci jama’a da su koma bakin ayyukansu yayin da ya umurce su da su ci gaba da ba yan sanda da sauran hukumomin tsaro bayanai kan ayyukan miyagu a garuruwansu.

Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Bankuna Uku, Sun Tafka Barna a Jihar Kogi

A baya mun kawo cewa wasu da ake zaton 'yan fashi da makami ne ɗauke da bindigu sun farmaki rassan bankuna uku, UBA, Zenith da kuma First Bank a yankin Ankpa, jihar Kogi, inda suka kwashi kuɗi iya son ransu.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da miji ya kai karar matarsa saboda ya sake ta amma ta ki barin gidansa

Yan Fashin, adadin mutum 20, an ce sun shiga garin da misalin ƙarfe 2:00 na rana. Da farko suka farmaki bankin UBA, daga nan suka zarce Bankin Zenith, daga bisani suka mamaye First Bank.

Daily Trust ta ruwaito wani da lamarin ya faru a idonsa na cewa maharan sun shiga garin kan ƙananan Motoci, Bas-Bas da Babura.

Asali: Legit.ng

Online view pixel