Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Bankuna Uku, Sun Tafka Barna a Jihar Kogi

Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Bankuna Uku, Sun Tafka Barna a Jihar Kogi

  • Wasu 'Yan bindiga da ake kyautata zaton 'yan fashi ne sun farmaki bankuna uku, sun kwashi makudan kuɗi a jihar Kogi
  • Wani mazaunin Ankpa, garin da lamarin ya faru yace maharan sun kai harin ne kan motoci ƙanana, Bas-Bas da Babura
  • Har yanzun babu cikakken bayani kan ko harin ya taɓa wani amma mazauna sun ce an shafe sama da awa guda

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kogi - Wasu da ake zaton 'yan fashi da makami ne ɗauke da bindigu sun farmaki rassan bankuna uku, UBA, Zenith da kuma First Bank a yankin Ankpa, jihar Kogi, inda suka kwashi kuɗi iya son ransu.

Yan Fashin, adadin mutum 20, an ce sun shiga garin da misalin ƙarfe 2:00 na rana. Da farko suka farmaki bankin UBA, daga nan suka zarce Bankin Zenith, daga bisani suka mamaye First Bank.

Kara karanta wannan

2023: 'Yan Bindiga Sun Buɗe Wa Mutane Wuta a Wurin Taron Jam'iyyar Siyasa, Sun Aikata Ɓarna

Reshen First Bank.
Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Bankuna Uku, Sun Tafka Barna a Jihar Kogi Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Daily Trust ta ruwaito wani da lamarin ya faru a idonsa na cewa maharan sun shiga garin kan ƙananan Motoci, Bas-Bas da Babura.

Shaidan ya bayyana cewa bayan fashi a Bankunan uku da masu POS mafi kusa, maharan sun kwashe kusan awa guda suna cin karen su babu babbaka. Yace yan bindigan sun fita garin suna harbi kan mai uwa da wabi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Sun fita garin ta kan Titin Okpo, amma babu wanda ya iya leƙo wa daga cikin gida domin maharan sun buɗe wuta ba ƙaƙƙauta wa. Mafi yawan mazauna Ankpa har yanzun suna ɓoye basu fito ba," Inji shaidan.

Shin an rasa rayuka a harin?

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton babu tabbacin ko akwai wanda ya rasa rayuwarsa sanadiyyar harin.

"Ba zamu ce kai tsaye babu wanda harin ya taba ba, harin ya kwashe sama awa guda," Inji wani mai suna Ahmed, mazaunin garin Ankpa, kamar yadda jaridar Sahara Reporters ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Bana Son Saɓa Wa Allah' Mata Ta Nemi Saki A Kotun Musulunci, Miji Yace Ta Biya Miliyan N1.6m Ya Saketa

Wani mazaunin kuma ya faɗa mana cewa bayan yan bindigan sun gama aiwatar da nufinsu, rundunar haɗin guiwa ta jami'an tsaro suka nufi yankin da lamarin ya faru.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sanda reshen jihar Kogi, SP William Aya, bai ɗaga kiran waya ko amsa sakonnin da aka tura masa kan lamarin ba.

A wani labarin kuma 'Yan Sanda Sun Yi Gumurzu da Yan Bindiga, Sun Ceto Dan Takarar PDP a jihar Katsina

Gwaraazan jami'an yan sanda a jihar Katsina sun kubutar da ɗan takarar kujerar majalisar jiha karkashin inuwar PDP a Kankiya.

Mai magana da yawun yan sanda, SP Gambo Isah, ya tabbatar da nasarar bayan gumurzu da maharan da daren Asabar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel