Wani Matashi Ya Koma Jami'ar Da Yayi Karatu, Yace Su Bashi Kudinsa Su Karbi Kwalinsu

Wani Matashi Ya Koma Jami'ar Da Yayi Karatu, Yace Su Bashi Kudinsa Su Karbi Kwalinsu

  • Wani bidiyon wani mutumi a jihar Oyo ya janyo cece-kuce a kafafen ra'ayi da sada zumunta
  • Matashin ya tafi jami'ar da ya kammala karatu idan ya bukaci hukumar makarantar ta amshi kwalinsa ta dawo masa da kudin makaranta
  • Mutane da dama sun bayyanawa cewa halin da matasa a Najeriya ke ciki ya tsananta matuka

Wani matashi da ba gano sunansa ba har yanzu ya bayyana a wani bidiyo inda ya tada tarzoma a jami'ar fasahar Ladoke Akintola dake Ogbomosho, jihar Oyo.

Matashin wanda a jami'ar ya kammala karatunsa ya mayar da kwalin digirinsa inda ya bukac jami'ar ta dawo masa da dukkan kudaden da ya biya na karatu.

Yace ya bukaci a dawo masa da kudinsa ne saboda tun da ya kammala karatu kwalin da ya samu bata amfanar da shi komai ba kuma yana cikin halin kakanikaye.

Kara karanta wannan

Tura ta kaI bango: Daliban Najeriya sun gaji da yajin ASUU, sun tura wani sako ga Buhari

A cewarsa:

"Ku bani kudina, ina cikin wahala." Mutumin ya bayyana a bidiyon da Linda Ikeji ta wallafa.

Kalli bidiyon:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shin me zai tursasa matashin yin haka

A farko shekarar nan, Statisa ta sakin rahoton rashin aikin yi tsakanin mata a 2022.

Rahoton ya nuna cewa alkaluman rashin aikin yi ya tashi daga 32.5% zuwa 33%.

Hakazalika a 2020, cibiyar kididdiga ta Najeriya NBS, tace kimanin masu kwalin doktora, 38,000 basu da aikin yi ko kuma suna ayyukan da bai kai matsayin mutuncinsu ba.

Matasan Najeriya kulli yaumin na guduwa zuwa kasashen wajen domin nemawa kans ayyukan yi.

Kalli ra'ayin jama'

Abdullahi Ibrahim Abbas:

Shikenan, tafaru takare, sai su amsa kwalinsu shikuma yabiyasu lokacin da suka dauka na koyamashi ababen daya koya, kuma ya Maida masu abinda suka koya mai.

Kara karanta wannan

Jami'ar Arewa ta yi watsi da ASUU, ta ce malamai su gaggauta dawowa bakin aiki

Jibrin Mohammed:

Wallahi Banga laifinsa, shegiya Boko sai kayi shekaru wajen 10 Kana ta Kame Kame Yadda zaka kammala, sai Ka kammala Zaka gane kuranka.

Muhammad Almanzili Alqadiry:

Hahaha wa ya gaya masa ana karatu ne dan aikin gwamnati ai kayi karatu dan wayiwa a rayuwa da sanin yakamata dakuma wasu damarmakin da zasu zo maka a awani wajan ya kama samari suyi kokari wajan sana oeh daban daban

Rabiu Uba Danzainab:

Kaji dan gari Allah wllh su baka kayanka kazo na sarar ma da salima cake kafara siyar wa

Zulaihat Lawal:

Allah sarki hala baisamu ai Kinyi bane da kwalin,Amma Ina hannunsa da kafa da Fasahar da Allah Yabashi?Yanzun wane yake jiran wani kwali

Abba Sauna Kawaji:

Allah sarki yaji kebur kenan.
Matasa kudaure kunemi koda qaramar sana'a ce.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel