Bidiyon Yadda Wani Ango Ya Yiwa Amaryarsa Yayyafin Kudi Bandir-bandir A Wajen Budan Kai Ya Ja Hankali

Bidiyon Yadda Wani Ango Ya Yiwa Amaryarsa Yayyafin Kudi Bandir-bandir A Wajen Budan Kai Ya Ja Hankali

  • Bidiyon wasu sabbin ma’aurata ya yadu a shafukan soshiyal midiya kuma ya kayatar da mutane matuka
  • An gano angon a tsaye yana yiwa kyakkyawar amaryarsa yayyafin kudi bandir-bandir a yayin shagalin budan kai
  • Ita kuma amarya Zainab Bello wacce ta sha ado ta kasance zaune da kanta duke tana mai murmushi

Soyayya ruwan zuma! Jama’a sun tofa albarkacin bakunansu bayan bayyanar bidiyon wasu sabbin ma’aurata a shafukan soshiyal midiya.

A makon jiya ne aka yi bikin angon mai suna Bassim da kyakkyawar amaryarsa Zainab Bello.

Amarya da ango
Bidiyon Yadda Wani Ango Ya Yiwa Amaryarsa Yayyafin Kudi Bandir-bandir A Wajen Budan Kai Ya Ja Hankali Hoto: northern_hypelady
Asali: Instagram

Kamar yadda yake bisa al’adan mallam Bahaushe akan yi budan kan amarya bayan an mika ta ga dangin mijinta.

Hakan ce ta kasance a bangaren wadannan sabbin ma’aura inda amarya da ango suka halarci wannan shagali cikin ado da kwalliya da ke bayyana tsantsar kyawu da kwarjininsu.

Kara karanta wannan

Bidiyoyi: Shigar Kasaita Da Fulani Ruqayya Bayero Tayi A Wajen Dinan Bikinta

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cikin bidiyon da shafin northern_hypelady ya wallafa a Instagram, an gano amarya Zainab zaune fuskarta lullube da mayafi yayin da ango Bassim ya iso wajen don bude kan amaryar tasa.

Sai dai da isarsa wajen, angon wanda ke cike da farin ciki ya fito da bandir-bandir din kudi yan dari biyar-biyar yana yiwa amaryarsa yayyafinsu, yayin da ita kuma ta sinne kai kasa tana mai murmushi mai sanyaya zuciya.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

folo_kom ta yi martani:

"Ubangiji sai yaushe oooo."

ummeeeytarh ta ce:

"Awwwwwww ma'auratana na mako."

zee__liman ta ce:

" Allah ya albarkaci auren."

kizzbeebah22 ta rubuta:

"❤️."

Bidiyoyin Yadda Shagalin Auren Ruqayya Bayero Ya Gudana A Fadar Sarkin Kano, An Yi Budan Kai

A wani labarin kuma, mun ji cewa daga karshe an mika diyar mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, Fulani Ruqayya zuwa dakin mijinta.

Kara karanta wannan

Neman Na Goro: Bidiyon Kyakkyawar Baturiya Tana Tallan Gyada A Titin Lagas Ya Yadu

A ranar Lahadi, 4 ga watan Satumba ne aka sada Gimbiya Ruqayya da sabon danginta a masarautar Kibiya.

An dai shafe kimanin mako guda ana ta shagali a masarautar Kano kama daga Lugude, Kunshi, Gada, Kamu, Kidan kwarya da sauransu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel