Neman Na Goro: Bidiyon Kyakkyawar Baturiya Tana Tallan Gyada A Titin Lagas Ya Yadu

Neman Na Goro: Bidiyon Kyakkyawar Baturiya Tana Tallan Gyada A Titin Lagas Ya Yadu

  • Bidiyon wata matashiyar baturiya tana tallan gyada a tsakiyan titin Lagas ya bayyana a shafukan soshiyal midiya kuma mutane da dama sun tofa albarkacin bakunansu
  • An gano matar sanye da atampa dinkin doguwar riga da faranti daure a kanta yayin da take bin motoci da gudu
  • Mutane da dama sun yaba kyawun matar yayin da wasu ke ganin ta yi hakan ne kawai don nishadi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Lagas - Jama’a sun yi cece-kuce kan bidiyon wata kyakkyawar baturiya tana tallan gyara a tsakiyan titin Lagas inda aka samu cunkoson ababen hawa.

Baturiyar ta sanya atampa dinkin doguwar riga da faranti daure a kanta yayin da take tallata haajarta ga matafiya da direbobi.

Baturiya
Neman Na Goro: Bidiyon Kyakkyawar Baturiya Tana Tallan Gyada A Titin Lagas Ya Yadu Hoto: TikTok/@majiq.pia
Asali: UGC

Wani bangare na bidiyon ya nunota tana zantawa da wani direba wanda ke son siyan haajarta. Direban ya tambayi kudaden gyadar, inda ta amsa cewa N500 ne.

A wani wurin kuma, an ganota da gudu tana bin wata farar mota da ke dauke da wani kwastoma. Sai da mutumin ya fada mata ta daina gudu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An bayyana matar a bidiyon na TikTok da suna Majiq Pia kuma ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya ta hanyar yin abun da yan Najeriya suka saba yi.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama’a sun yi martani

priscadaniel511 ya ce:

“Kun gani ko kun ace mata kada ta yi gudu da yawa idan dan Najeriya ne za ku cewa mai shi yayi gudu mana.”

@Naaaaaa ya ce:

“Wato babu wanda zai yi magana game da mutumin cikin motar bas da yace “kada ki yi gudu.”

shizydiamond ya ce:

“Hakan ya yi kyau mutanena na son turawa za su siye komai cikin kankanin lokaci.”

Dan Allah Ki Kamani: Matashi Ya Rude Da Ganin Kyakkyawar Yar Sanda, Mutane Sun Rirrike Shi

A wani labarin, wani matashi a kasar Birtaniya ya nadi wani bidiyo da ke nuna lokacin da ya hadu da wata kyakkyawr jami’ar yar sanda a wajen wani shagalin biki.

A cikin bidiyon, matashin yana ta ihun “ki kamani dan Allah”. Jami’ar yar sandan ta murmusa sakamakon yabon da take ta samu daga matashin dan farar hula.

Jim kadan bayan ya fara nadan bidiyon, ya nunawa mutane yadda jami’ar yar sandan ta yi kyakkyawan shiga mai daukar hankali wanda ya fito da tsantsar kyawunta. Matashiyar ta kasa daina yin dariya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel