Bidiyoyin Yadda Shagalin Auren Ruqayya Bayero Ya Gudana A Fadar Sarkin Kano, An Yi Budan Kai

Bidiyoyin Yadda Shagalin Auren Ruqayya Bayero Ya Gudana A Fadar Sarkin Kano, An Yi Budan Kai

  • A makon jiya ne masarautar Kano ta aurar da diyarta, Fulani Ruqayya Aminu Bayero ga angonta Amir Kibiya
  • An dai sha shagulgula iri-iri a wannan biki kama daga Lugude, Gada, Kamu, Kunshi da dai sauransu
  • A ranar Lahadi, 4 ga watan Satumba ne aka rufe bukin da liyafar budan kai bayan an mika amarya ga sabon danginta a masarautar Kibiya

Kano - Daga karshe an mika diyar mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, Fulani Ruqayya zuwa dakin mijinta.

A ranar Lahadi, 4 ga watan Satumba ne aka sada Gimbiya Ruqayya da sabon danginta a masarautar Kibiya.

Sarkin Kano, diyarsa da angonta
Bidiyoyin Yadda Shagalin Auren Ruqayya Bayero Ya Gudana A Fadar Sarkin Kano, An Yi Budan Kai Hoto: fashionseriesng
Asali: Instagram

An dai shafe kimanin mako guda ana ta shagali a masarautar Kano kama daga Lugude, Kunshi, Gada, Kamu, Kidan kwarya da sauransu.

Kara karanta wannan

Hotunan: Haifaffiyar Jihar Kano Ta Zama Lauya A Manyan Kotunan Ingila Da Wales

Dubban jama'a sun shaida daurin auren Ruqayya da angonta Amir Kibiya a ranar Juma’a, 2 ga watan Satumba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cikin bidiyoyi da hotunan da suka yadu a soshiyal midiya, an gano inda amarya ta yi bankwana da mahaifinta tana mai zub da hawaye yayin da shi kuma ya dafa kanta don sanya mata albarka.

Bayan ta yi bankwana da masarautar Kano zuwa ta Kibiya, an gudanar da kasaitaccen shagalin budan kai a ranar Lahadi.

Kamar kodayaushe, amarya ta fito shar da ita cikin kasaitaccen shiga na leshi

Kalli bidiyon shagalin a kasa:

Bidiyoyi: Shigar Kasaita Da Fulani Ruqayya Bayero Tayi A Wajen Dinan Bikinta

A baya mun kawo cewa a ranar Juma’a 2 ga watan Satumba ne aka daura auren diyar sarkin Kano, Ruqayya Aminu Bayero da angonta dan sarkin Kibiya, Amir Kibiya. '

Kara karanta wannan

Bidiyoyi: Shigar Kasaita Da Fulani Ruqayya Bayero Tayi A Wajen Dinan Bikinta

A yayin da ake shirin rufe bikin, an gudanar da wani hadadden liyafar dina a daren yau Asabar, 3 ga watan Satumba.

Amarya ta yi kasaitaccen shiga da ado na kece raini inda ta sanya wata hadaddiyar doguwar riga da aka yiwa ado da duwatsu masu walwali sannan daga baya an yi masa wani rufi tamkar alkyabba irin na ‘ya’yan sarauta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel