Bidiyoyi: Shigar Kasaita Da Fulani Ruqayya Bayero Tayi A Wajen Dinan Bikinta

Bidiyoyi: Shigar Kasaita Da Fulani Ruqayya Bayero Tayi A Wajen Dinan Bikinta

  • Alkawari dai ya cika tsakanin Fulani Ruqayya Aminu Bayero da angonta Amir Kibiya inda aka daura masu aure a ranar Juma'a
  • Domin rufe shagulgulan da aka shafe kimanin mako guda ana yi, an shirya wani kasaitaccen liyafar dina a yau Asabar
  • Amarya Gimbiya ta yi wani hadadden shiga ta kece raini inda tuni bidiyoyinta suka yadu a shafukan soshiyal midiya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kano A ranar Juma’a 2 ga watan Satumba ne aka daura auren diyar sarkin Kano, Ruqayya Aminu Bayero da angonta dan sarkin Kibiya, Amir Kibiya.

Tun a karshen makon jiya ne aka fara shagulgulan bikin inda aka gudanar da bukukuwan al’ada irin su Lugude, kunshi, Gada da sauransu.

A yayin da ake shirin rufe bikin, an gudanar da wani hadadden liyafar dina a daren yau Asabar, 3 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Hotuna da Bidiyon shagalin Gaɗa da aka yi na bikin Gimbiya Ruƙayya Bayero

Ruqayya Bayero da Amir Kibiya
Bidiyoyi: Shigar Kasaita Da Fulani Ruqayya Bayero Tayi A Wajen Didan Bikinta Hoto: fashionseriesng/weddingpostng
Asali: Instagram

Amarya ta yi kasaitaccen shiga da ado na kece raini inda ta sanya wata hadaddiyar doguwar riga da aka yiwa ado da duwatsu masu walwali sannan daga baya an yi masa wani rufi tamkar alkyabba irin na ‘ya’yan sarauta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A daya daga cikin bidiyoyin shagalin da suka yadu a shafukan soshiyal midiya, an gano lokacin da amarya da ango da kuma wani dan uwansu suka shigo dakin taron cike da kasaita da kwarjini irin na jinin sarauta.

Kalli bidiyoyin a kasa:

Kano: Masu Fadi a Ji Sun Dira Auren Diyar Sarki Aminu Bayero da 'Dan Sarkin Kibiya

A baya mun ji cewa kwaryar birinin Kano ta cika ta batse a ranar Juma'a yayin da 'dan sarkin Kibiya, Alhaji Umar Usman ya auri diyar Sarkin Kano, Rukayya Aminu Bayero inda manyan mutane suka halarci daurin auren.

Kara karanta wannan

Yajin Aiki: Ɗan El-Rufai Ya Ce ASUU 'Bata Da Amfani', An Masa Zafafan Martani

Jim kadan bayan addu'o'in, Dr Abdullahi Umar Ganduje wanda ya tsaya matsayin waliyyin amarya, yayi addu'ar Allah ya albarkaci auren tare da basu yara nagari.

An daura auren a fadar Sarkin Kano tare da gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje wanda ya bayar da auren kan sadaki N200,000.

Asali: Legit.ng

Online view pixel