Jihohin Najeriya 10 Da Mata Suka Fi Kwankwaɗar Barasa, Kamfanonin Giya Sun Samu N542bn Cikin Wata 6

Jihohin Najeriya 10 Da Mata Suka Fi Kwankwaɗar Barasa, Kamfanonin Giya Sun Samu N542bn Cikin Wata 6

 • Duk da tsadar rayuwa a kasar, da alamu wasu yan Najeriya ba su shirya dena siyan wasu abubuwa da suke kauna ba
 • Alkalluma sun nuna cewa a cikin watanni shida, yan Najeriya sun kashe fiye da Naira biliyan 542 wurin siyan ababen sha
 • An kuma bayyana jerin jihohi 10 da aka fi shan giyan tare da jihar da mata suka fi sha

A cikin watanni shida na farkon shekarar 2022 yan Najeriya sun siya lemun kwalba da giya wanda kudinsu ya kai Naira biliyan 599.11.

Hakan na nuna cewa an samu karin kashe 31.2 cikin 100 idan aka kwatanta da Naira biliyan 456.44 da aka kashe a watannin farkon 2021.

An gano adadin kudaden da aka kashe ne a bayanin kudi na kamfanonin Nigeria Breweries, Guinness, International Breweries da kuma Champion Brew da aka tura wa Nigerian exchange.

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan bindiga sun sako wata tsohuwa mai shekaru 90 da aka sace a jirgin Kaduna

Mata na shan abun sha
Jihohin Najeriya 10 Da Mata Suka Fi Shan Barasa A Yayin Da Kamfanonin Giya Suka Samu N542bn Cikin Watanni 6. Credit: Klaus Vedfelt.
Asali: Getty Images

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Nigerian Breweries

A cewar rahoton Nigerian Breweries, a watannin shida na farkon shekara, mutane sun kashe Naira biliyan 24.03 wurin siyan hajojinsu.

Wasu daga cikin abubuwan da suke siyarwa sun hada da 33 Export lager beer, Williams dark ale, Turbo Kings, Maltex, Hi Malt da wasu.

Guinness

A bangarensa, kamfanin Guinness ya sayarwa yan Najeriya abubuwan sha na Naira biliyan 206.82. Fitattun hajojin da kamfanin ke sayarwa sun hada da Guinness Stout, Guinness Gold, Snapp, Origin da Dubic Malt.

International Breweries

Kamfanin da ke yin Castle Milk Stout, Castle Lager, Redds, Hero, Grand Malt da Voltic Water sun sayar da haja ta Naira biliyan 111/40 a wata shida.

Champion Brew

Kamfanin mallakan Heineken, Champion Brew ta ce ta samu kudin shiga har Naira biliyan 6.86 cikin watanni shida.

Wasu daga cikin abubuwan sha da suka siyarwa sun hada da Champion Lager Beer da Champ Malta.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga suka kashe fitaccen lauya a Zamfara

Jihohi 10 inda mata suka fi shan giya

Hakazalika, wani rahoto daga hukumar kididdiga ta kasa, NBS ya nuna jihohin da suka fi yawan mata da ke shan giya a Najeriya.

Rahoton wanda, wanda aka fitar daga hadin gwiwa tsakanin NBS da Bankin Duniya, UNICEF da wasu hukumomin ya nuna cewa mata daga jihar Cross Rivers a lokacin tattara rahaton su kan sha giya a kalla sau daya kowanne wata.

Jihohin da mata suka fi shan giyan sune:

 • Cross River
 • Imo
 • Bayelsa
 • Delta
 • Ondo
 • Rivers
 • Enugu
 • Abia
 • Akwa Ibom
 • Ogun

Shan giya ba zai hana ka shiga Aljanna ba, tana magani: Limamin Cocin Katolika

A wani rahoton, wani malamin addinin Kirista a Najeriya, Father Oluoma Chinenye John, ya yi tsokaci mai daukan hankali game da shan giya da yasa yan Najeriya da dama suka fara tafka muhawara.

A cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Instagram, malamin addinin ya bayyana cewa shan giya dai-dai misali ba zunubi bane idan har mutum ba ya rika sha fiye da kima.

Kara karanta wannan

Mazauna a Kaduna sun fusata, sun sheke wata wata mai boye 'yan bindiga a gidanta

Asali: Legit.ng

Online view pixel