Shan giya ba zai hana ka shiga Aljanna ba, tana magani: Limamin Cocin Katolika

Shan giya ba zai hana ka shiga Aljanna ba, tana magani: Limamin Cocin Katolika

  • Wani fasto a Najeriya, Fada Oluoma Chinenye John, ya bayyana cewa shan giya ba zunubi bane
  • Da ya ke yi wa mutanen cocinsa wa'azi, ya fada musu cewa shan giya na yin magani a jiki kuma ba zai hana su zuwa aljanna ba
  • Wasu yan Najeriya da dama sun yi martani a kan bidiyon, sun ce sun yarda da shi cewa bai kamata a hana shan giyan dai-dai gwargwado ba

Wani malamin addinin Kirista a Najeriya, Father Oluoma Chinenye John, ya yi tsokaci mai daukan hankali game da shan giya da yasa yan Najeriya da dama suka fara tafka muhawara.

A cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Instagram, malamin addinin ya bayyana cewa shan giya dai-dai misali ba zunubi bane idan har mutum ba ya rika sha fiye da kima.

Kara karanta wannan

Na saci Baibul ne don in karanta in kuma yaɗa kalmar Ubangiji, wanda ake zargi ya fada wa kotu

Shan giya ba zai hana ka shiga Aljanna ba, tana da magani: Limamin Cocin Katolika
Shan giya ba zai hana ka shiga Aljanna ba, tana da magani: Fada Oluoma. Hoto: @fadaoluoma
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mambobin cocinsa sun yi mamaki

Ya cigaba da cewa shan giyan ma yana maganin wasu cutattuka kuma Baibul na goyon bayan shan giyan. Mambobinsa da ke sauraronsa sun natsu sosai wasu daga cikinsu kuma akwai alamar mamaki a fuskarsu.

Ya ce:

"Duk abin da Allah ya hallita, kamar giya, idan ka sha dai-dai misali, zai maka amfani."

Har wa yau, Fada Oluoma ya bukaci mambobin cocinsa su cigaba da shan giyansu, su dena tsoron hakan zai taba musu addininsu.

Ga bidiyon a kasa:

A lokacin hada wannan rahoto, kimanin mutane 800 sun yi tsokaci kan bidiyon sannan mutum fiye da 7,000 sun latsa masa like kamar yadda Adeola Fayehun ta sake wallafawa.

Legit.ng ta tattaro martanin wasu mutane:

emmycomedy_arena ya ce:

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Halin da ake ciki kan batun ɗan uwan Goodluck Jonathan da yan bindiga suka sace

"Mun baka kwalban Henny guda daya fasto."

dylancalisto ya ce:

"Shi kansa Yesu ya sauya ruwa zuwa giya."

blazingchic ta ce:

"Menene abin muhawara? Idan baka shan giya, kada ka sha. Idan kana so, ka sha amma dai-dai kima. Tana iya shafan lafiya ... shi ke nan. Na san wasu da ke yi kamar Whiskey da vodka daga wuta suke amma suka sha Palm Wine, wane suke yaudara?."

jessylove_220 ta ce:

"Mu'ujizar da Yesu ya yi na farko ita ce sauya ruwa zuwa giya, ko a Baibul, Ubangiji bai taba hana shan giya ba, kawai ya hana sha da yawa ne."

Asali: Legit.ng

Online view pixel