Shugaban ASUU Ya Bayyana Hadarin da Zai Biyo Bayan Hana Su Albashin Watanni 6

Shugaban ASUU Ya Bayyana Hadarin da Zai Biyo Bayan Hana Su Albashin Watanni 6

  • Shugaban kungiyar ASUU na kasa baki daya ya maida martani ga kalaman da Ministan ilmi ya yi a game da yajin-aikin malamai
  • Adamu Adamu ya shaida cewa gwamnatin tarayya ba za ta biya malamai albashin lokacin da suka shafe su na yajin-aiki ba
  • Farfesa Emmanuel Osodeke yace muddin aka ki biyan su bashin albashinsu na watanni shida, dalibai ne za su yi asarar karatunsu

Abuja - Kungiyar ASUU ta malaman jami’ar Najeriya tace ba za ta janye yajin-aikin da take yi ba, har sai an biya ta bashin albashin da ta ke bin gwamnati.

Punch ta ce shugaban ASUU na kasa, Emmanuel Osodeke ya shaida mata wannan a ranar Alhamis, 18 ga watan Agusta 2022, a jawabin martani da ya fitar.

Hakan na zuwa ne bayan gwamnatin tarayya tace ba za ta biya malaman jami’an albashin watanni shida da suka wuce ba, domin ba su koyar da dalibai ba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari: Ya kamata daliban jami'a su maka ASUU a kotu, su nemi diyyar bata lokaci

Farfesa Emmanuel Osodeke yake cewa Ministan ilmi yana wasa ne, domin kuwa idan har ba a biya su duk kudinsu ba, ba za su koyar da daliban jami’a ba.

Shugaban na ASUU yake cewa idan wannan salo gwamnati ta dauka, malamai ba za su koyar dalibai na zangon da ake ciki kafin a rufe makarantun kasar ba.

Ayi dai mu ga ni inji ASUU

“Wasa yake yi, idan ba su biya ba, ba za mu koyar da daliban nan ba; ba za mu biya bashin karatun wannan lokaci ba

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Za mu fara sabon zango ne na 2022/2023. Ba za mu gudanar da jarrabawa ba; za mu cigaba da sabon zagon karatu."
Ministan ilmi
Ministan ilmi, Malam Adamu Adamu Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Mu ba irin Likitoci ba ne

“Malaman jami’a ba kamar Likitoci ba ne da idan aka rasa rai, shikenan ba zai dawo ba. Malamai za su iya komawa, a biya asarar da aka yi.

Kara karanta wannan

Ba Za a Bude Jami’o’i Kwanan nan ba, ASUU Tayi Magana Kan Dogon Yajin-Aikinta

Amma idan suka ki biyanmu kudinmu, to ba za mu fanshe lokacin da aka rasa ba. Kuma ba za mu biyan bashin ayyukan da suka taru ba.
Za a fara sabon zango, 2022/20223. Ba za ayi jarrabawa ko a koya darasin lokacin da ya wuce ba.”

- Emmanuel Osodeke

Babu aiki babu kudi - Babu kudi babu aiki

An rahoto Osodeke yana cewa idan gwamnati ba za ta biya su albashi sai sun yi aiki ba, su ma malamai ba su yi aiki a jami’o’i ba har sai an biya su albashi.

Shugaban ASUU ya karasa zancensa da cewa Malam Adamu Adamu, bai san abin da yake fada ba.

Minista yace ba a cika alkawari ba

A gefe guda, an ji labari Ministan harkokin lantarki ya tabbatar da cewa ba a cika alkwarin da aka yi ba. Abubakar Aliyu yace wutar lantarki na ja baya.

A watan Yuli ne Gwamnatin da Muhammadu Buhari yake jagoranta ta sha alwashin kara karfin lantarkin da ake da shi zuwa 5000mw, har yau ba a dace ba.

Kara karanta wannan

Karfin hali: Dalibin kwaleji ya yI barazanar sace 'Provost', ya shiga hannun hukuma

Asali: Legit.ng

Online view pixel