Ba Za a Bude Jami’o’i Kwanan nan ba, ASUU Tayi Magana Kan Dogon Yajin-Aikinta

Ba Za a Bude Jami’o’i Kwanan nan ba, ASUU Tayi Magana Kan Dogon Yajin-Aikinta

  • Shugaban kungiyar ASUU na kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke ya yi magana kan bude jami’o’i
  • ASUU ta zargi Gwamnatin Muhammadu Buhari, tace ba da gaske take yi domin a koma aiki ba
  • Wani ‘dan majalisar NEC na ASUU bai dauki zaman karshe da aka yi a matsayin taron kwarai ba

Nigeria – Jaridar The Cable ta rahoto kungiyar ASUU ta malaman jami’o’in Najeriya ta bayyana cewa yajin-aikin da ake yi ba zai kare nan kusa ba.

Shugaban kungiyar ASUU na kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke ya yi jawabi a ranar Laraba, 17 ga watan Agusta 2022 game da batun yajin-aikin na su.

Premium Times ta shirya wani taro a dandalin Twitter, aka gayyaci Farfesa Emmanuel Osodeke domin ya yi wa mutanen Najeriya karin haske.

An yi tunanin yajin-aikin zai zo karshe a zaman da ASUU tayi da gwamnatin tarayya a yammacin Talata, amma kuma zaman bai haifar da da mai ido ba.

Kara karanta wannan

Daliban Jami’a Sun Ki Daukar Shawarar Minista, Za Su Kai Gwamnati kotu kan ASUU

Ba a zo da komai ba

Shugaban na ASUU yake cewa gwamnatin Najeriya ba ta nuna niyyar biyawa malaman jami’a bukatunsu ba, wadanda suka jawo aka daina karatu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Emmanuel Osodeke ya fada a taron da aka yi a Twitter cewa gwamnati ba ta zo masu da komai ba.

ASUU.
Emmanuel Osodeke da Chris Ngige Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Abin ya kara muni a yau - ASUU

“Lamarin yanzu ya fi muni a kan lokacin da mu ka soma. Gwamnatin tarayya ba ta nuna wani kokarin yadda za ta sa kudi a jami’o’i da harkar ilmi ba.”
“Su na ta ikirarin ba su da kudi, babu wanda zai yarda da haka. Babu kudi amma mutum daya ya saci N109bn, gwamnati na neman sasantawa da shi?”
“Gwamnati ba ta nuna da gaske take yi ba.”

- Farfesa Emmanuel Osodeke

Farfesan yake cewa abin takaici ne a ce an rufe jami’o’in kasar nan, amma babu abin da ke gaban masu mulki zai yadda za a lashe zabe mai zuwa a 2023.

Kara karanta wannan

Buhari ga jami'ai: Ku tabbata kun kawar 'yan ta'addan Najeriya gaba daya

An dawo da maganar kwamitin Briggs

Kamar yadda Vanguard ta kawo rahoto, ASUU tace ba ta dauki zaman da aka yi da gwamnatin tarayya na ranar Talata a matsayin wani taron kirki ba.

Daya daga cikin ‘yan majalisar NEC na ASUU, Farfesa Moyosore Ajao yace babu abin kirkin da aka zo da shi, sai ma aka dawo da kwamitin Nimi Briggs.

Yajin-aiki ya kai wata 6

Malaman jami’a sun shafe sama da watanni shida su na yajin-aiki a fadin kasar nan. Daliban jami’o’in gwamnatin tarayya su na gida tun a Fubrairu.

Dama tun farko an ji labari cewa Kungiyar ASUU ta malaman jami’a tayi barazanar cewa idan aka garkame jami’o’im to sai lokacin da Allah ya yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel