Saura shekara 1 a Mulki, Minista Ya Ambaci Dalilin Gaza Cika Alkawarin Lantarki

Saura shekara 1 a Mulki, Minista Ya Ambaci Dalilin Gaza Cika Alkawarin Lantarki

  • Ministan harkokin lantarki ya koka game da yadda karfin wuta yake kara sauka kasa a Najeriya
  • A maimakon wutan da ake samu ya karu, Injiniya Abubakar Aliyu yace abin kara lalacewa yake yi
  • Aliyu yace karancin gas ya jawo ake fama da wannan matsala, ya yi alkawarin magance matsalar

Abuja - Ministan harkokin wutar lantarki, Abubakar Aliyu yace matsalar gas ta jawo gwamnatin tarayya ta gaza samar da megawatt 500 na lantarki.

A maimakon wutar lantarki ya karu a Najeriya, Premium Times ta rahoto Ministan yana mai cewa abin ya kara ja baya ne a yanzu maganar da ake yi.

A ranar Laraba, karfin wutar lantarkin da ake da shi ya sauka zuwa megawatt 4100. Abubakar Aliyu ya bayyana wannan bayan taron FEC a Abuja.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari: Ya kamata daliban jami'a su maka ASUU a kotu, su nemi diyyar bata lokaci

Aliyu ya shaidawa manema labarai cewa gwamnatin Muhammadu Buhari ba ta cika alkawarin da tayi a watan Yuli na ganin an samar da 5000mw ba.

An yi alkawari, an gagara cikawa

“Mun fada maku a ranar 1 ga watan Yuli za mu kara karfin wuta zuwa 5000mw lokacin da aka kawo kwangila.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Amma ba mu iya yin wannan ba, saboda matsaloli da suka shafi kwangilolin gas da mu ke kokarin magancewa."
FEC Aso Villa
Ana taron FEC a Abuja Hoto: Buhari Sallau
Asali: Twitter

Abin yana yin baya ne - Minista

Kamar yadda This Day ta kawo rahoto, a ranar Talata akwai 4600mw, amma adadin ya ragu zuwa 4100, ranar da aka yi taron majalisar zartarwa na kasa.

Ministan tarayyar yace babu yadda ma’aikatarsa za iya da batun gas, don haka ya sanar da ‘Yan Najeriya cewa wuta za ta rika yin yawo a kwanakin nan.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ma'aikatan Lantarki A Najeriya Sun Dakatar Da Yajin Aiki Bayan Ministan Kwadago Ya Zauna Da Su

Duk da kalubalen da ake fuskanta, Ministan lantarkin ya nuna ana sa rai nan gaba abubuwa su yi kyau, domin ana kokarin ganin karfin karfin wutan ya karu.

A jawabin da ya yi, Aliyu ya yi albishir da labarin N2,740,000,000 da majalisar FEC ta amince da shi domin biyan diyya ga mutanen da za a kora a Zungeru.

Ina N18bn suka shiga?

Shugaban kwamitin kudin gwamnati, Hon. Oluwole Oke ya bada labarin cewa sun gano an fitar da N18bn da sunan share daji a karkashin ma'aikatar gona.

Bayan bincike da aka soma, an ji cewa ‘Yan majalisa ba su gamsu an yi wadannan kwangiloli ba, don haka suka gayyaci kamfanonin su bayyana a gabansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel