TCN Ta Roki Ma’aikatan Wutar Lantarki Su Hakura, Kada Su Shiga Yajin Aiki

TCN Ta Roki Ma’aikatan Wutar Lantarki Su Hakura, Kada Su Shiga Yajin Aiki

  • Ma'aikatan wutar lantarki sun yi barazanar fadawa yajin aikin sai baba ta gani saboda wasu dalilai
  • Hukumomi sun shiga damuwa, sun fara kira ga ma'aikatan da su hakura su manta da batun shiga yajin
  • Wannan yaji dai na zuwa ne daidai lokacin da gwamnatin Buhari ke ci gaba da kai ruwa rana da ASUU

FCT, Abuja - Kamfanin wutar lantarki na Najeriya (TCN), ya yi kira ga ma’aikatan wutar lantarki da su dakatar da yunkurin yajin aikin da suke shirin farawa a ranar 17 ga watan Agusta, Daily Nigerian ta ruwaito.

Manajan Daraktan TCN, Dokta Sule Abdulaziz ne ya yi wannan roko a cikin wata wasika da ya aike wa ma’aikatan a ranar Talata, biyo bayan barazanar da suka yi na shiga yajin aikin domin warware bukatunsu.

Kara karanta wannan

A shirye muke: ASUU sun sauko, sun ce za su iya janye yaji a yau bayan ganawa da FG

TCN na rokon ma'aikata kada su shiga yajin aiki
TCN Ta Roki Ma’aikatan Wutar Lantarki Su Hakura, Kada Su Shiga Yajin Aiki | Hoto: gazettengr.com
Asali: UGC

Ma’aikatan da ke karkashin kungiyar ma’aikatan wutar lantarki ta kasa (NUEE), a ranar 15 ga watan Agusta, sun umurci mambobinsu da su mamaye ofisoshin TCN a fadin kasar a ranar 16 ga watan Agusta, daga nan kuma za su fara yajin aiki a ranar 17 ga watan Agusta.

Dalilin yajin aiki

Rahotonmu na baya ya bayyana dalilin da yasa ma'aikatan za su fara wannan yaji na sai baba ta gani.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Babban Sakataren (NUEE), Joe Ajaero ya ce sun dauki matakin ne domin nuna rashin amincewarsu da umarnin da TCN ta bayar na cewa duk manyan Manajojin da ke rike da mukamin mukaddashin Manaja dole ne su bayyana don tattaunawar karin girma.

Mista Joe Ajaero, ya ce umarnin ya saba wa yanayin aikin ma’aikata da kuma hanyoyin ci gaban sana’arsu, kuma ya yi zargin cewa an yi hakan ne ba tare da masu ruwa da tsaki na ma'aikatan ba, rahoton People Gazette.

Kara karanta wannan

Bayan Wata 4 rak a Ofis, An Soma Yunkurin Raba Adamu da Shugabancin APC

Sauran batutuwan da aka tabo sun hada da cin mutuncin ma’aikata daga ofishon gwamnatin tarayya da kuma rashin biyan tsoffin ma’aikatan PHCN hakkokinsu na watan Disamba 2019.

Amma Dr Abdulaziz ya ce kamfanin ya dakatar da "tattaunawar da aka ambata… yayin da muke kammala tattaunawa da hukumar."

Har ila yau, Karamin Ministan Makamashi, Goddy Jedy-Agba, a wata wasika mai dauke da kwanan watan 15 ga watan Agusta, 2022 ga kungiyar, ya ce ma’aikatar ta dukufa wajen samar da mafitar da za a amince da ita a duk bangarorin da abin ya shafa.

A cewarsa:

"Muna kira ga babbar kungiyar da ta ba mu makonni biyu daga ranar wannan wasikar don magance matsalolin tare da samar da shawarwari don daidaita duk wasu batutuwa."

Kyakkyawan Labari Ga Daliban Najeriya, ASUU Ta Ce Za Ta Gana da FG Kan Batun Janye Yajin Aiki

A wani labarin, kwanaki dari da tamanin da uku bayan da mambobin kungiyar malaman jami’o’i suka fara yajin aikin, shugabanninsu na shirin sake ganawa da tawagar gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan

Rikici Ya Barke Tsakanin Kungiyar Yarbawa Na OPC Da Dillalan Shanu A Jihar Kwara

Shugaban kungiyar na kasa, Emmanuel Osodeke a ranar Litinin, 15 ga watan Agusta, ya bayyana cewa ASUU za ta gana da FG domin shawo kan matsalolin da suka shafi yajin aikin a yau Talata 16 ga watan Agusta.

Da yake magana a gidan talabijin na Channels TV a shirin Politics Today, ya ce kungiyar a shirye ta ke ta janye yajin aikin da zarar gwamnatin Buhari ta biya bukatar ta a ganawar da aka shirya gudanarwa a yau.

Asali: Legit.ng

Online view pixel