Kyakkyawan Labari Ga Daliban Najeriya, ASUU Ta Ce Za Ta Gana da FG Kan Batun Janye Yajin Aiki

Kyakkyawan Labari Ga Daliban Najeriya, ASUU Ta Ce Za Ta Gana da FG Kan Batun Janye Yajin Aiki

  • Shugaban kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ya ba da tabbacin cewa kungiyar za ta janye yajin aikin da take yi nan da nan IDAN gwamnatin tarayya ta biya bukatun ta
  • Emmanuel Osodeke ya tabbatar da cewa akwai shirin ganawa tsakanin gwamnatin Najeriya da shugabannin kungiyar ASUU a ranar Talata 16 ga watan Agusta
  • A cewar Osodeke, tsarin biyan albashi na IPPIS FG ke kakabawa ‘ya’yan kungiyar na komai bane illa shirin cutar dasu

Kwanaki dari da tamanin da uku bayan da mambobin kungiyar malaman jami’o’i suka fara yajin aikin, shugabanninsu na shirin sake ganawa da tawagar gwamnatin tarayya.

Shugaban kungiyar na kasa, Emmanuel Osodeke a ranar Litinin, 15 ga watan Agusta, ya bayyana cewa ASUU za ta gana da FG domin shawo kan matsalolin da suka shafi yajin aikin a yau Talata 16 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

A karo na biyu: Buhari ya tura sako mai daukar hankali ga ASUU, ya fadi abin da yake so su yi

Akwai yiwuwar ASUU ta janye yaji
Kyakkyawan Labari Ga Daliban Najeriya, ASUU Ta Ce Za Ta Gana da FG Kan Batun Janye Yajin Aiki | Hoto: nairametrics.com
Asali: UGC

Da yake magana a gidan talabijin na Channels TV a shirin Politics Today, ya ce kungiyar a shirye ta ke ta janye yajin aikin da zarar gwamnatin Buhari ta biya bukatar ta a ganawar da aka shirya gudanarwa a yau.

A kalamansa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Idan muka shiga waccar ganawar gobe kuma gwamnati ta ce, abin da kuka daidaita a kai, a shirye muke mu sanya hannu, za a janye yajin aikin.

ASUU ta bayyana IPPIS a matsayin tsagwaron yaudara

Jaridar Punch ta ruwaito cewa tun farko Osodeke ya yi Allah-wadai da shirin kwange da damfara da gwamnatin Najeriya ke shirin daura mambobin kungiyar a kai.

Da yake tsokaci kan kin amincewa da tsarin tsarin biyan albashin ma’aikata na bai daya (IPPIS) da kungiyar ta yi, Osodeke ya yi gargadin cewa IPPIS yaudare ce da gwamnati ta shirya.

Kara karanta wannan

Fitaccen lauya ga su Dangote: Ku taimaki ASUU kamar yadda kuka taimaka a lokacin Korona

Ya kara da cewa:

"Mun dade muna ta ihun cewa IPPIS yaudara ce, mun shaida musu cewa shekara 16 suna kwashe kudinmu da IPPIS, sun kuntatawa mambobinmu saboda haka."

A Karo Na Biyu, Shugaba Buhari Ya Sake Rokon ASUU Su Yi Hakuri Su Janye Yajin AikI

A wani labarin, yayin da kungiyar malaman jami'o'i suka shafe akalla watanni bakwai suna yaji, shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya bukaci su hakura su janye yajin.

Rahoton da muka samo ya bayyana cewa, Buhari ya bayyana hakan ne a taron bikin karrama Alhaji Muhammadu Indimi, shugaban kamfanin Oriental Energy Resources Ltd a birnin Maiduguri na jihar Borno.

An gudanar da wannan babban taro ne a cikin jami'ar Maiduguri, daya daga cikin manyan makarantun Najeriya da ke garkame sakamakon yajin ASUU.

Asali: Legit.ng

Online view pixel