An Kashe Mutane Hudu Yayin da Rikici Ya Barke Tsakanin OPC da Dillalan Shanu a Kwara

An Kashe Mutane Hudu Yayin da Rikici Ya Barke Tsakanin OPC da Dillalan Shanu a Kwara

  • An kashe mutane a wata arangama da ya barke tsakanin dilolin shanu da yan kungiyar kabilar yarbawa na OPC
  • Yansandan jihar kwara ta ce buge fitilar daya daga cikin ayarin motocin da ya dauko mambobin OPC da shanun wani bafulatani yayi ya janyo rikici
  • Hukumar yansanda ta ce adadin mutanen da aka kashe a rigimar Fulani da yan OPC ya kai hudu

Jihar Kwara - Akalla mutane hudu ne suka mutu a wata arangama tsakanin dilolin shanu da yan kungiyar kabilar yarbawa na OPC a Ajase dake karamar hukumar Irepodun ta jihar Kwara, a ranar Juma’a. Rahoton Daily Trust

Ba a san ainihin abin da ya janyo rikicin ba amma majiyoyin daban-daban sun bada labarin abin da suka sani game da rikicin.

Kara karanta wannan

Bilkisu Mai Gadon Zinari: Bidiyon Yadda Aka Ciccibo Wata Amarya A Kan Wani Kasaitaccen Gado Kamar Na Sarauta

Wata majiya ta ce rikicin ya fara ne a lokacin da wata mota dake jigilar yan kungiyar OPC ya kusa buge wani bafulatani dillalin shanu a lokacin da yaje tsallaka titi.

Fushi yasa bafulatani ya far ma daya daga cikin yan kungiyar OPC daga bisani sauran mambobin OPC dake cikin motan suka afka masa da duka, suka masa taron dangi inji majiyar.

cowsw
An Kashe Mutane Hudu Yayin da Rikici Ya Barke Tsakanin OPC da Dillalan Shanu a Kwara FOTO Legit.NG
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Ajayi Okasanmi ya fitar, ya tabbatar da faruwar lamarin amma ya ce adadin wadanda suka mutu ya kai hudu.

Ya kara da cewa rikicin ya barke ne bayan wata saniya ta lalata madubin motar da ke dauke da mambobin OPC a lokacin da suke wucewa ta hanyar kasuwar Kara dake jihar Kwara.

Mambobin kungiyar OPC suna cikin ayarin motoci kusan ashirin da ake kyautata zaton sun fito ne daga bikin Osun Osogbo na jihar Osun.

Kara karanta wannan

“Saboda Zafin Rana, Turawa Sun Gudu”: Dan Najeriya Ya Nuna Yadda Tituna Suka Zama Wayam A Turai

Ajayi ya ce hakan ya haifar da cece-kuce wanda daga karshe ya kai ga yin musayar wuta tsakanin yan kungiyar OPC da kuma dillalan shanu a kasuwar wanda yayi sanadiyar kashe mutane hudu.

Ya ce an dawo da zaman lafiya yakin yayi da aka baza jami’an yan sanda domin dakile tabarbarewar doka da oda.

Abu Uku Da Zan Mayar Da Hankali A Kai Idan Na Zama Gwamnan Kaduna - Isa Ashiru

A wani labari kuma, Honorabul Isa Ashiru Kudan, dan takarar gwamna jihar Kaduna Jam'iyyar PDP ya bayyana abubuwa guda uku da za mayar da hankalin sa idan ya zama gwamna. Rahoton BBC

Ashiru Kudan wanda ke takarar gwamnan jihar Kaduna karo na uku yace abun na farko da zai fara ba muhimmanci a jihar shine fannin tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa

Online view pixel