Bayan Wata 4 rak a Ofis, An Soma Yunkurin Raba Adamu da Shugabancin APC

Bayan Wata 4 rak a Ofis, An Soma Yunkurin Raba Adamu da Shugabancin APC

  • Wasu sun bijiro da cewa akwai bukatar Shugaban Jam’iyyar APC ya bar kujerar da yake kai
  • Abullahi Adamu ne Shugaban APC, kuma Jam’iyyar ta tsaida Musulmi-Musulmi a takarar 2023
  • Akwai masu ganin ya kamata Sanata Adamu ya yi waje domin a lallashi Kiristoci da ke APC

Abuja - Ana jita-jitar cewa an samu sabanin shugabanci a jam’iyyar APC mai mulki a matakin kasa, har ta kai wasu su na maganar a canza shugaba.

Rahoton da Vanguard ta fitar a ranar Litinin 15 ga watan Agusta 2022 ya nuna wasu daga cikin masu ruwa da tsaki suna neman tsige Abdullahi Adamu.

Sanata Abdullahi Adamu ya shiga ofis a matsayin sabon shugaban jam’iyyar APC na kasa ne a karshen watan Maris, bai yi watanni biyar da fara aiki ba.

Kara karanta wannan

Wasu Shugabannin PDP na Neman Tada Rikici, Sun ce An Ware Su a Yakin Zaben Atiku

Kamar yadda jaridar ta fada, wasu daga cikin ‘ya ‘yan APC mai mulki su na korafi a game da irin rikon da Sanata Abdullahi Adamu yake yi wa jam’iyyar.

Labari ya fara canzawa

Da farko abin kai ga maganar sauke shugaban jam’iyyar ba, amma yanzu abubuwa sun fara rikida, biyo bayan tsaida 'yan takarar shugabancin Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A karshen makon da ya wuce, wasu daga cikin jagororin APC na kasa suka fara kokarin ganin yadda za ayi waje da Adamu daga kujerar da yake kai.

Abdullahi Adamu
Abdullahi Adamu wajen bikin kaddamar da Shettima Hoto: OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Masu wannan yunkuri sun zo da wannan shiri ne domin lallashi kiristocin jam’iyyar da ke ganin an hana su kujerar ‘dan takarar shugaban kasa a 2023.

Wani jagora a jam’iyyar ya zanta da Vanguard ba tare da ya yarda ambaci sunansa ba, inda yace an bijiro da batun ne saboda ayi wa kowa adalci a tafiyar.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Wasu Sabbin Hotuna Daga Aso Villa Sun Nuna Tinubu Na Kus-Kus da Mataimakin Buhari

Majiyar tace baya ga kujerar shugaban jam’iyya, ana so Kirista ya zama shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, an fara kawo sunan Hon. James Faleke.

Tun da aka ba Musulmai tikitin takarar shugaban kasa da mataimaki a zabe mai zuwa, wasu suke ganin dacewar shugaban APC ya bar matsayinsa.

An samu matsalar kudi a jam'iyya

Bayan haka, an kawo rahoto a Nairaland cewa ana zargin Adamu da kin maida hankali kan zaben 2023, sanan ba a biya ma’aikatan jam’iyya albashinsu ba.

Wani zargin da ake yi wa Adamu shi ne har yanzu ba a gama magance rigingimun cikin gida ba, sannan an ki maidawa ‘yan takara kudn fam da suka biya.

Atiku ba bukatar 'Yan Kudu

An ji labari tsohon Gwamna kuma jagora a jam’iyyar hamayya, Bode George ya gargadi Atiku Abubakar a kan takarar shugabancin Najeriya da zai yi.

George yace ba zai yiwu Atiku Abubakar ya zama Shugaban kasa, PDP ta koma fadar Aso Villa, ba tare da ya samu kuri’u daga mutanen Kudancin Najeriya ba.

Kara karanta wannan

Baba-Ahmed Ya Gargadi Yan Najeriya Akan Su Guje Wa Yan Takara Masu Nuna Kabilanci da Addini a Zaben 2023

Asali: Legit.ng

Online view pixel