An Cafke Mutumin Da Ya Kai Yan Mata Otel, Ya Sace Musu iPhone 6 Bayan Zuba Musu Maganin Barci Cikin Abin Sha

An Cafke Mutumin Da Ya Kai Yan Mata Otel, Ya Sace Musu iPhone 6 Bayan Zuba Musu Maganin Barci Cikin Abin Sha

  • Rundunar yan sandan Najeriya reshen Jihar Legas ta kama wani Ifeanyi Ezennaya kan zarginda da satar wayoyin salula na yan mata da wasu kayayyaki
  • Bincike ya nuna cewa Ezennaya yana yaudarar yan mata ne ya kai su dakin otel sannan ya saka musu sinadarin barci a abin sha kayin ya yi musu fashi
  • SP Benjamin Hundeyin, mai magana da yawun yan sandan Jihar Legas ya tabbatar da kama wanda ake zargin ya kuma ce kawo yanzu ba a gano wayoyin ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Legas - Yan sandan jihar Legas sun kama wani mutum mai shekaru 36, Ifeanyi Ezennaya, kan zargin sace wa mata shida wayoyinsu na iPhone da kudinsu ya kai N4m bayan shayar da su kwaya.

Kamfanin Dillancin Labarai na kasa, NAN, ta rahoto cewa lamarin ya faru ne a ranar Talata a Falolu Street, Surulere Legas, The Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Har Yanzu Ni Dan Gani Kashe Nin Buhari Ne, In Ji Fasinjan Da Aka Ceto Daga Jirgin Kasar Kaduna Zuwa Abuja

Wanda ake zargi da sace wa yan mata iPhone
An Cafke Mutumin Da Ya Kai Yan Mata Otel, Ya Sace Musu iPhone 6 Bayan Zuba Musu Maganin Barci Cikin Abin Sha. Hoto: @thecableng.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ezennaya, ya kai yan matan Otel ne sannan ya saka wani sinadari da ba a sani ba cikin abin shansu sannan ya sace musu wayoyi da sauran ababe masu daraja.

Daya daga cikin yan matan da abin ya faru da ita ta shaidawa NAN cewa ta hadu da shi ne kwanaki kadan da suka wuce wurin bikin bazday din kawarta.

Wasu daga cikin yan matan sun magantu

"Mun hadu da shi a mashaya, ya taho wurin mu ya gabatar da kansa ya ce sunansa Emeka, ya yi ikirarin bai dade da dawowa ba daga Switzerland kuma yana son mu zama abokai.
"Mu biyu muka bashi lambar waya.
"A ranar Talata, ya kira mu ya ce mu tafi otel mu shakata, muka yarda.
"Ya kai mu dakin da ya riga ya biya.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: An Kashe Yan Sanda 4, An Kona Motocci A Harin Da Yan Bindiga Suka Kai Caji Ofis

"Ya fito da giya da wasu ababen sha daga firinji ya zuba mana, shikenan abin da za mu iya tunawa," in ji ta.

Wata daban ta ce da suka farka bayan awa shida ba su gan shi ba.

"Mun sha giyan misalin karfe 7 na yamma, mun farka 10 na safe muka ga an sace mana iPhones shida, agogo, sarkar gwal da wasu abubuwa.
"A lokacin ne muka gane an saka mana kwaya a abin sha," in ji ta.

Yan sanda sun kama wanda ake zargin a wani otel a ranar Alhamis a Allen Avenue, Ikeja inda ya ke shirin yi wa wata macen fashi.

Martanin yan sanda

Kakakin yan sandan Legas, SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da labarin ya ce wanda ake zargin yana shayar da matan kwaya ne sannan ya sace kayansu.

A cewarsa har yanzu ba a gano wayoyin ba.

Katsina: 'Yan sanda sun kama wani da ke yaudarar mata ya kwana da su a otel ya kuma sace musu waya da kuɗi

Kara karanta wannan

Har gara 2015: Kasar nan na cikin ha’ula’i, ba a ga komai ba sai 2023 inji Sanusi II

A wani rahoton, jami'an yan sanda a Jihar Katsina sun kama wani mutum mai shekaru 31 da ake zargin yana amfani da intanet wurin yaudarar mata yana kwanciya da su a Kano, Vanguard ta ruwaito.

An shaida wa manema labarai cewa wanda ake zargin, Usama Tijjani, mazaunin Daurayi Quaters ne a karamar hukumar Gwale a Jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel