Har Yanzu Ni Dan Gani Kashe Nin Buhari Ne, In Ji Fasinjan Da Aka Ceto Daga Jirgin Kasar Kaduna Zuwa Abuja

Har Yanzu Ni Dan Gani Kashe Nin Buhari Ne, In Ji Fasinjan Da Aka Ceto Daga Jirgin Kasar Kaduna Zuwa Abuja

  • Hassan Usman, wani lauya da ke cikin fasinjojin jirgin kasar Abuja zuwa Kaduna da yan bindiga suka sace ya ce har yanzu yana cikin masoyan Shugaba Buhari
  • Usman ya shafe kimanin kwanaki 100 a hannun yan bindigan kuma yana cikin wadanda yan bindigan suka saki bidiyo inda suke yi musu bulala kafin a ceto su
  • Amma kuma lauyan ya bayyana cewa gwamnatin na Shugaba Muhammadu Buhari bata sauke nauyin da ke kanta ba na kare rayuka da dukiyoyin yan kasa duk da kudin da ake kashewa kan tsaro

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Daya daga cikin wadanda aka ceto daga harin jirgin kasar Abuja-Kaduna, Hassan Usman, ya ce har yanzu shi dan gani kashe nin Shugaba Muhammadu Buhari ne, The Punch ta rahoto.

Kafin sakinsa a ranar 25 ga watan Yuli, Usman, wanda lauya ne, da matarsa Amina suna cikin fasinjojin da aka sace yayin harin ranar 28 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

An Cafke Mutumin Da Ya Kai Yan Mata Otel, Ya Sace Musu iPhone 6 Bayan Zuba Musu Maganin Barci Cikin Abin Sha

Train Abductee.
Har Yanzu Ni Dan Gani Kashe Nin Buhari Ne, In Ji Fasinjan Da Aka Ceto Daga Jirgin Kasar Kaduna Zuwa Abuja. Hoto: @thecableng.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Usman ya shafe fiye da kwanaki 100 a hannun yan ta'adda kuma yana cikin wadanda aka gani a bidiyo yan ta'adda na yi musu bulala.

Da ya ke magana da ICIR, Usman ya ce duk da cewa har yanzu yana goyon bayan Buhari, a bangaren tsaro gwamnatin ta ci maki 'kasa da 50 cikin 100'.

"Saboda daya cikin manyan hakokin gwamnati shine kare rayyuka da dukiyoyin yan kasa.
"Amma a yanzu, zan iya cewa gwamnati bata tabuka komai ba a wannan bangaren. Duk da kudade mai yawa da aka ware wa tsaro, babu wani abin da aka tsinana."

Da ya ke magana kan halin da ya shiga, Usman ya ce ya sha bakar wahala don sunyi tafiya a kasa na tsawon kwana uku kafin suka isa sansanin yan bindiga.

Kara karanta wannan

'Ni Na Rika Yi Wa Yan Bindiga Magani,' Fasinjar Jirgin Kaduna Da Ya Samu Yanci Ya Magantu

Ya ce bayan sun isa sansanin ba su samun isashen barci kuma a kasa suke kwana cikin ruwa da rana ga kuma sauro da macizai da kunamu da wasu dabobin da ke cizonsu.

Buhari: Mun Ba Wa Jami'an Tsaro Cikakken 'Yanci Su Kawo Karshen Ta'addanci

A wani rahoton, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa ta bawa hukumomin tsaro 'cikakken dama' domin kawo karshen hare-hare a kasar.

A cikin sanarwar da Garba Shehu, kakakin shugaban kasa ya fitar, Buhari ya bayyana hare-haren da aka yi a Sokoto, Plateau da Kaduna a matsayin 'tsageranci'.

Buhari, wanda ya mika ta'aziyya ga iyalan wadanda abin ya faru da su, ya tabbattarwa gwamnatin jihohi cewa gwamnatinsa za ta cigaba da yin duk abin da ya dace don inganta tsaro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel