Wike Ya Gayyaci Jigon APC, Wamakko, Ya Kaddamar Da Ayyuka A Rivers

Wike Ya Gayyaci Jigon APC, Wamakko, Ya Kaddamar Da Ayyuka A Rivers

  • Gwamnan Jihar Rivers Nyesom Wike ya gayyaci Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko zuwa birnin Port Harcourt don kaddamar da tituna da ya gina
  • Tsohon gwamnan na Jihar Sokoto kuma jigo a jam'iyyar APC mai mulki ya tabbatar da cewa an tura masa takardar gayyatar bikin kaddamar da ayyukan da za a yi ranar 9 ga watan Agusta
  • Gwamna Wike yana daga cikin masu karfin fada a ji a jam'iyyar hamayya ta PDP kuma ya yi takarar neman tikitin kujerar shugaban kasa a zaben 2023 amma ya sha kaye hannun Atiku Abubakar

Gwamna Nyesom Wike ya gayyaci jagoran jam'iyyar APC a Jihar Sokoto, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, ya zo ya kaddamar da ayyuka a Jihar Rivers a ranar 9 ga watan Agusta, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Atiku ya ba da Dino Malaye babban matsayi a tawagar kamfen dinsa

Takardar gayyatar na dauke da kwanan watan 2 ga watan Agusta kuma tana dauke da sa hannun gwamnan.

Sanata Wamakko.
Wike Ya Gayyaci Jigon APC, Wamakko, Ya Kaddamar Da Ayyuka A Rivers. Hoto: @daily_trust.
Asali: Facebook

A cikin wasikar, Wike ya gayyaci tsohon gwamnan Jihar Sokoton, wanda shine shugaban kwamitin tsaro na Majalisa, don kaddamar da tagwayen titin Ogbumnmu-abali a Port Harcourt.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wike jigo ne a babban jam'iyyar hamayya, ta Peoples Democratic Party, PDP.

Ya yi takarar neman tikitin kujerar shugaban kasa a zaben 2023 amma ya sha kaye hannun Atiku Abubakar kuma ya ki daukansa matsayin mataimaki.

Wike ya yi musayar maganganu da tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku tun lokacin yayin da shugabannin jam'iyyar ke kokarin sulhunta su.

Wasikar ta ce:

"Gwamnatin Jihar Rivers ta kammala ginin tagwayen hanya na Ogbumnu-abali a birnin Port Harcourt a wani bangare na shirin sabunta birni da cigaban jihar.

Kara karanta wannan

Rikicin siyasa: Tsigaggen mataimakin gwamnan PDP ya ja zuga, masoyansa sun koma APC

"Za a kaddamar da titin a hukumance a ranar 9 ga watan Agustan 2022 misalin karfe 11 na safe.
"Don haka ina gayyatar ku domin zuwa kaddamar da titunan, kamar yadda aka tsara, da izinin Allah da kuma amfanin mutanen Jihar Rivers.
"Mun gode, duk da cewa ba a sanar da wuri ba, mai girma, muna gaisuwa da girmamawa, kamar yadda aka saba."

Sanata Wamakko ya tabbatar da cewa ya samu takardar gayyatar a hirar waya da ya yi da wakilin Daily Trust.

2023: Rikicin PDP Ya Dauki Sabon Salo, Gwamnoni Da Ke Goyon Bayan Wike Sun Gindayawa Atiku Sabbin Sharruda

A wani rahoton, gwamnonin jam'iyyar PDP da ke biyaya ga gwamnan Rivers, Nyesom Wike, sun bada wasu sharruda ga dan takarar shugaban kasa Atiku Abubakar, kafin su mara masa baya a zaben 2023, kamar yadda aka rahoto.

A cewar Daily Independent, gwamnonin za su hadu da Atiku a karshen mako don tattaunawa kan matsalolin da ke adabar jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Zai iya yin abin da ya ga da: FG ta fadi dalilin da yasa Buhari zai ba 'yan Nijar motocin N1.5bn

Jaridar ta rahoto cewa daya daga cikin mambobin tawagar Gwamna Wike yana cewa duk ma abin da ya faru, sun amince babu wanda zai fita daga jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel