Zai yi abin da yake so: FG ta ba dalilin da yasa Buhari zai ba jamhuriyar Nijar motocin N1.5bn

Zai yi abin da yake so: FG ta ba dalilin da yasa Buhari zai ba jamhuriyar Nijar motocin N1.5bn

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince a dauki motoci na makudan miliyoyi a ba jamhuriyar Nijar
  • Wannan lamari ya tunzura 'yan Najeriya, an fara cece-kuce tare da neman dalilin kashewa kasar waje kudi
  • Gwamnati ta yi magana, ta bayyana dalilin da yasa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yanke wanna shawara

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya, a ranar Laraba, ta kare kudurin shugaban kasa Muhammadu Buhari na kashe Naira biliyan 1.145 ga Jamhuriyar Nijar, Daily Trust ta ruwaito.

Ministar Kudi, Kasafin da Tsare-Tsare ta Kasa Zainab Ahmed, ta yi wannan tsokaci ne a lokacin da ta ke gabatar da tambayoyi bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya da shugaban kasa ya jagoranta a fadar gwamnati da ke Abuja.

Shugaba Buhari ya ba 'yan Nijar kyautar motoci
Zai yi abin da yake so: FG ta ba dalilin da yasa Buhari zai ba jamhuriyar Nijar motocin N1.5bn | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Ministar, wacce ta ce shugaban kasar na da ‘yancin yanke shawara don amfanin Najeriya, ta kara da cewa "wannan ba shi ne karon farko da kasar ke ba da irin wannan gudunmawa ga makwabtanta ba."

Kara karanta wannan

Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Ya Koka Kan Tsadar Rayuwa, A Yayin Da Farashin Kayayyaki Ke Cigaba Tashi A Kasar

Ta ce shugaban kasar na da hurumin daukar irin wadannan shawarwari bayan ya yi nazari a tsanake.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewarta, gwamnatin Najeriya ta sha ba da irin wannan tallafi ga kasashe kamar su Kamaru, Nijar da ma Chadi, Vanguard ta ruwaito.

A fadinta:

“Shugaban kasar ya yi nazarin abubuwan da ake bukata bisa bukatar shugabanninsu. An amince da irin wadannan bukatun kuma ana ba da gundunmawar.
“An yi hakan ne don inganta karfinsu na kare kasashensu, kamar yadda ya shafi tsaro da kuma Najeriya."

Ta kara da cewa:

“Yan Najeriya na da ‘yancin yin tambayoyi, amma kuma shugaban kasa shi ma yana da alhakin tantance abin da zai amfani kasar nan, kuma ni kaina ba zan iya kalubalantar hukuncin ba.
“Na fada wannan ba shi ne karon farko ba kuma Najeriya a matsayin kasa ta ba da taimako ga makwabtanmu. Yin haka shi ne mafi alheri ga Najeriya.”

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Ana ta batun hana acaba, FRSC za ta fara kame wasu nau'ikan babura a Najeriya

Wani rahoto a baya ya nuna cewa shugaba Buhari ya amince da ba da motoci kirar Toyota Land Cruiser kusan guda 10 ga ‘yan jamhuriyar Nijar, amma bai bayyana dalilin yin hakan ba.

Buhari Zai Raba Tallafin N38bn ga ‘Yan Najeriya Miliyan 1.9, ga Jihohin da Za Su Samu

A wani labarin, gwamnatin Buhari ta shirya cire 'yan Najeriya akalla miliyan biyu daga kangin talauci ta hanyar raba musu N20,000 kowane a karkashin shirin tallafawa marasa galihu.

Rahoton da Legit.ng Hausa ta samo ya gano cewa, shirin na zuwa ne a karkashin ma'aikatar jin kai, kuma tuni an tattara bayanan bankin wadanda za su ci gajiyar shirin.

Sadiya Umar Faruk, minstan ma'aikatar ta jin kai tuni aka ce ta fara raba kudaden ga mazauna babban birnin tarayya Abuja, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel