Rikicin siyasa: Bayan tsige shi, magoya bayan mataimakin gwamnan PDP sun koma APC

Rikicin siyasa: Bayan tsige shi, magoya bayan mataimakin gwamnan PDP sun koma APC

  • ‘Yan majalisar dokokin jiha sun tsige mataimakin gwamnan Oyo Injiniya Rauf Aderemi Olaniyan a ranar Litinin, 18 ga watan Yuli
  • Sai dai wannan lamari ya haifar da abubuwa da dama a jam'iyya mai mulki a jihar da kuma manyan jiga-jiganta
  • A baya-bayan nan dai shi ne aka ga ficewar wadanda suke goyon bayan tsigagge Olaniyan ta hanyar shiga jam’iyya mai mulki ta APC

Jihar Oyo - Magoya bayan Rauf Olaniyan da aka tsige daga matsayin mataimakin gwamnan jihar Oyo, sun sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa jam'iyyar APC a karamar hukumar Iseyin, kamar yadda Daily Independent ta ruwaito.

Hakan ya faru ne a daidai lokacin da ‘yan kungiyar Unity Forum na APC suka bayyana cewa sun yi Makinde ne a zaben 2019 saboda Olaniyan.

Kara karanta wannan

Hausawan Arewacin Najeriya na cikin zaman dar-dar a Imo yayin da IPOB suka kashe 'yan Nijar 8

Masoya tsohon mataimakin gwamnan Oyo sun koma APC tare dashi
Rikicin siyasa: Bayan tsige shi, magoya bayan mataimakin gwamnan PDP sun koma APC | Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Sun gana da dan takarar gwamna, Teslim Folarin

Sun bayyana hakan ne a ranar Talata, 2 ga watan Agusta, a lokacin da Teslim Folarin, dan takarar gwamna na jam'iyyar APC da Olaniyan suka ziyarci garin tare da wasu jiga-jigan jam'iyyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lateef Kolawole, wanda tsohon shugaban karamar hukumar Iseyin ne ya tabbatar wa da shugabannin jam’iyyar APC ba da goyon bayansu domin ganin APC ta samu nasara a zaben 2023 mai zuwa. .

Yace:

"In sha Allahu za mu rubanya kokarinmu na "aikin lallasa PDP a zaben 2023" kuma ba za mu yi ruwa da tsaki don ganin tsohon garin Iseyin da kewaye ya samawa jam'iyya mai ci gaba ba nasara."

A halin da ake ciki, shugabannin kungiyar Unity Forum da suka magantu sun bayyana cewa sun zabi Makinde ne a zaben da ya gabata saboda Olaniyan, wanda a lokacin yana daya daga cikin mambobinsu.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Sakateriyar PDP ta dagule, ana ta kira ga tsige shugaban jam'iyya

Idan baku manta ba, an tsige mataimakin gwamnan ne saboda ficewa da ya yi daga jam'iyyar PDP yayin da yake kan aikinsa, rahoton Ripples Nigeria.

An tsige mataimakin gwamnan jihar Oyo daga kan kujerarsa

A wani labarin, rahotanni da ke zuwa mana sun kawo cewa an tsige mataimakin gwamnan jihar Oyo, Mista Rauf Olaniyan, daga kan kujerarsa.

Nigerian Tribune ta rahoto cewa an tsige Olaniyan ne bayan majalisar dokokin jihar ta amince da rahoton kwamitin mutum bakwai da babban alkalin kotu ya kafa don binciken zargin da ake yiwa mataimakin gwamnan na rashin da’a a zamanta na ranar Litinin.

Shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin jihar Oyo, Sanjo Adedoyin, ya ce an samu mataimakin gwamnan da dukka laifukan da ake zarginsa a kai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel