Sabon Sarki: Matasa sun yi a Zanga Zanga, sun Nemi Tinubu ya Takawa Abba Birki

Sabon Sarki: Matasa sun yi a Zanga Zanga, sun Nemi Tinubu ya Takawa Abba Birki

  • Yayin da wasu al'ummar Kano ke ta murnar sake nada Muhammadu Sunusi II a matsayin sarkin Kano, wasu matasa a Abuja sun tsunduma zanga-zangar nuna bacin rai
  • Matasan karkashin kungiyar concerned patriots of Nigeria sun yi tattaki zuwa fadar shugaban kasa da majalisa suna neman shugabanni su sa baki domin takawa gwamna Abba birki
  • Jagoran tafiyar Abdullahi Muhammed Saleh ya zargi gwamnatin Abba Kabir Yusuf da juya Kano domin bukatar kashin a wani yunkuri na muzgunawa tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- Nadin sabon Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II ya tayar da kura a babban birnin tarayya Abuja,yayin da wasu matasa suka fara zanga-zanga.

Kara karanta wannan

Sarki Muhammadu Sunusi II ya jagoranci sallarJuma'a a fadar Gwamnatin Kano

Tuni matasan suka tsunduma zanga-zanga har fadar shugaban kasa dake Aso Rock da harabar majalisar kasar nan suna neman a shiga lamarin.

Malam Muhammadu Sunusi II
Ana zanga-zangar rashin goyon bayan nadin Sarki Muhammadu Sunusi II a Abuja Hoto: Muhammadu Sunusi II
Asali: Twitter

An yiwa Abba zanga-zanga saboda nadin Sarki

The Nation ta wallafa cewa matasan rike da kwalaye sun bayyana damuwa kan yadda al'amura ke wakana a jihar Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A jiya ne dai Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da dokar sake fasalin masarautun Kano biyar da tsohon gwamnan jihar kuma shugaban APC a yanzu Abdullahi Ganduje ya samar.

A yau kuma aka tabbatarwa da Sarkin Kano na 14 Muhammadu Sunusi II karagarsa.

An zargi gwamna Abba da rashin kyautawa

Kungiyar matasa ta concerned patriots of Nigeria ta yi zanga-zanga tana neman Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tsawatarwa gwamna Abba Kabir Yusuf.

Jagoran tafiyar, Abdullahi Muhammed Saleh ya shaidawa manema labarai cewa dole sai manya sun tsawatar kan yadda ake siyasantar da sarautun gargajiya a Kano.

Kara karanta wannan

Ana zargin shi ya shirya komai, Kwankwaso ya yi magana kan tsige sarakunan Kano

Pulse Nigeria ta tattaro Abdullahi Muhammed Saleh na cewa bai kamata Gwamna Abba Kabir Yusuf ya rushe sarakuna biyar domin nada sarki daya ba.

Ya zargi gwamnan da gudanar da mulkin kama-karya tun bayan da ya sha rantsuwar kama aiki a bara.

Kungiyar ta yi zargin da gangan gwamnatin Abba Kabir Yusuf ke ayyukan da ba za su jefa Kano cikin mawuyacin hali.

Tsige sarakuna: Kwankwaso ya wanke kansa

Mun kawo muku labarin yadda jagoran darikar kwankwasiyya ta NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya wanke kan shi daga zargin ingiza gwamnatin Kano wajen tsige sarakunan masarautun jihar.

Sanata Kwankwaso na wannan batu ne yayin da wasu ke ganin da yawunsa aka tsige sarakunan, tare da nada Malam Muhammadu Sunusi II a matsayin sabon sarki mai daraja ta daya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.