Bidiyon Yadda Aka Yi Cinikin Fura Tsakanin Yan Uwan Amarya Da Abokan Ango A Wajen Bikin Fatima Garo

Bidiyon Yadda Aka Yi Cinikin Fura Tsakanin Yan Uwan Amarya Da Abokan Ango A Wajen Bikin Fatima Garo

  • Hausawa akwai su da al’adu masu ban sha’awa wanda ya banbanta shi da sauran mutane musamman a yayin shagalin aure
  • Bikin amarya Fatima Tijjani Sule Garo da angonta Mahi Salisu Ladan ya kayatar sosai domin an nuna wasu al'adu masu ban sha'awa
  • An dai yi cinikin fura tsakanin yan uwan amarya da abokan ango kafin aka basu damar ganin amaryarsu

Ko shakka babu Mallam Bahaushe na da al'adun masu ban sha'awa idan shagalin aure ya tashi, kama daga Kamu, wankar Amarya da dai sauransu.

Hakazalika a wuraren wannan bukukuwa a kan gudanar da yan wasanni na gargajiya domin kayatar da mahalarta taron musamman ma a tsakanin bangaren ango da amarya.

Hakan ce ta kasance a wajen wani kasaitaccen biki da aka yi na wata amarya mai suna Fatima Tijjani Sule Garo da angonta Mahi Salisu Ladan.

Kara karanta wannan

Ku Hana Su 'Yan Matanku Fitar Da Tsiraici Ranar Aurenku, Fasto Ya Shawarci Amaren Da Zasu Shiga Daga Ciki

Amarya da ango
Bidiyon Yadda Aka Yi Cinikin Fura Tsakanin Yan Uwan Amarya Da Abokan Ango A Wajen Bikin Fatima Garo Hoto: surykmata
Asali: Instagram

A wajen wannan biki, an yi wata dan barkwanci tsakanin yan uwan amarya da abokan ango kafin aka baiwa angon damar ganin amaryarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin wani bidiyo da MC Surykmata ta wallafa a shafinta na Instagram, an gano isowar ango da abokansa amma sai aka taka musu birki sannan aka hana su isa wajen da amaryar take zaune.

An kuma jiyo yan matan amaryar suna tambayan angwanen ko za su siya furan da suke siyarwa, daga nan dai aka yi ciniki inda abokan angon suka tattara damin kudi a cikin wani zani suka baiwa amaren.

Daga san sai ango ya isa ga amaryarsa wacce ke lullube da mayafi sannan ta mika masa yar tasa dauke da furan a ciki. Daga nan sai DJ ya saka masu kida don su dan taka.

Bidiyon Kayan Sa Lalle Na "Allah Amin" Da Dangin Ango Suka Kai Gidansu Fatima Shettima

Kara karanta wannan

El-Rufai: Buhari Bai Ma San Yan Ta'adda Sun Yi Barazanar Sace Shi Ba, Sai Da Na Sanar Da Shi

A wani labarin, mun ji cewa ana ci gaba da shagulgulan bikin Fatima Shettima, diyar tsohon gwamnan jihar Borno kuma dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar APC, Kashim Shettima.

Fatima da angonta Sadiq Ibrahim Bunu, zasu shiga daga ciki a ranar Asabar, 30 ga watan Yuli 2022 a garin Maiduguri, babbar birnin jihar Borno.

Kamar yadda yake bisa al’adar Arewa dangin ango kan hada kayayyaki na sa lalle sannan su kaiwa bangaren gidan amarya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel