Bidiyon Kayan Sa Lalle Na "Allah Amin" Da Dangin Ango Suka Kai Gidansu Fatima Shettima

Bidiyon Kayan Sa Lalle Na "Allah Amin" Da Dangin Ango Suka Kai Gidansu Fatima Shettima

  • Alkawarin Allah zai cika a tsakanin Fatima Kashim Shettima da angonta Sadiq Bunu a ranar 30 ga watan Yuli
  • Dangin ango sun kai kayan sa lalle na ganin na fada gidan su Fatima wacce ta kasance diyar tsohon gwamnan Borno
  • A cikin wani bidiyo da ya yadu, an gano akwatuna da kayan kwalam da makulashe da aka gabatarwa dangin amaryar na sa lalle

Ana ci gaba da shagulgulan bikin Fatima Shettima, diyar tsohon gwamnan jihar Borno kuma dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar APC, Kashim Shettima.

Fatima da angonta Sadiq Ibrahim Bunu, zasu shiga daga ciki a ranar Asabar, 30 ga watan Yuli 2022 a garin Maiduguri, babbar birnin jihar Borno.

Kamar yadda yake bisa al’adar Arewa dangin ango kan hada kayayyaki na sa lalle sannan su kaiwa bangaren gidan amarya.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Wani rahoton sirri ya fallasa, 'yan ta'adda sun tara makamai za su afkawa jihar Buhari

Fatima Shettima
Bidiyon Kayan Sa Lalle Na Kece Raini Da Dangin Ango Suka Kai Gidansu Amarya Fatima Shettima Hoto: weddingpostng
Asali: Instagram

Hakan ce ta kasance a bangaren Bunu domin sun shirya kayan sa lallai na kece raini sannan sun gabatar da shi a gidan surukarsu Fatima.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A wani bidiyo da shafin weddingpostng ya wallafa a Instagram, an gano wasu taron mata yan kai kayan lalle dauke da kayan makulashe Kwando-don da sauran abubuwa dangin su biskit, chakulet, lemuka katan-katan.

A gefe guda kuma an gano wasu setin akwati da aka cika da kayayyaki na alfarma.

Bidiyoyi Daga Shagalin Bikin Fatima Shettima Da Angonta Sadiq Bunu

A baya mun kawo cewa kamar yadda aka saba bisa al’adan bikin ‘ya’yan manya a Najeriya, tun a makon jiya ne aka fara gudanar da shagulgulan bikin Fatima Shettima.

Tuni dai aka fara bude taro da kasaitaccen liyafa ta Dina inda amarya da ango suka gaji da kyau tare da fitowa shar da su.

Kara karanta wannan

Fuskokin Wasu Daga Cikin Mutanen Da Yan Bindiga Suka Sace A Sabon Harin Kaduna

A daya daga cikin bidiyoyin da shafin blackswansazy ya wallafa a Instagaram, an gano amarya sanye da wata hadaddiyar doguwar riga fara irin ta amare kanta yane da lullubi inda ta tsaya ana ta daukarta hadaddun hotuna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel