Hotunan Abba Kyari a gaban kotu: Kotu ta ki amincewa da ba da belin DCP Abba Kyari

Hotunan Abba Kyari a gaban kotu: Kotu ta ki amincewa da ba da belin DCP Abba Kyari

  • Wata kotu a babban birnin tarayya ta yi zama, ta duba yiwuwar ba da belin DCP Abba Kyari da ake zargi da harkallar kwayoyi
  • Kotun ta ce ta duba batutuwa da dama da hukumar NDLEA ta gabatar, inda tace ta gamsu da nuna adawa da ba da belin nasa
  • Ana tuhumar Abba Kyari ne tare da wasu jami'ai bayan da bidiyo ya yadu da ke nuna suna kokarin kulla harkallar kwayoyi

Abuja - Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ki amincewa da bukatar neman belin da DCP Abba Kyari da mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, Sunday J. Ubua suka shigar.

Idan baku manta ba ana tuhumarsu da laifukan da suka shafi harkallar muggan kwayoyi tare da wasu mutane biyar, The Nation ta ruwaito.

Da dumu-dumu: Kotu ta ki amincewa da ba da belin DCP Abba Kyari kan batun harkallar muggan kwayoyi
Da dumu-dumu: Kotu ta ki amincewa da ba da belin DCP Abba Kyari | Hoto: Tvcnewsng
Asali: Facebook

Mai shari’a Emeka Nwite, a wani hukunci da ya yanke a safiyar yau Litinin, ya ce masu gabatar da kara sun gabatar da isassun hujjoji a gaban kotu domin nuna kin amincewa da belin manyan jami’an ‘yan sandan biyu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Jami'an gidan gyaran hali sun shirya a kotu domin tafiya da Abba Kyari

A maimakon haka, Mai shari’a Nwite ya ba da damar ci gaba da sauraron karar.

A baya dai lauyoyin Abba Kyari sun nemi a ba da belinsa saboda rashin lafiya da aka ce Abba Kyari na fama dashi, wanda hukumar NDLEA ta ce sam ba za ta amince ba domin Kyari zai iya guduwa.

Wasu hotunan da gidan talabijin na TVC ya yada ya nuna lokacin da Abba Kyari tare da sauran wadanda ake zargi ke zaune a bakin kotu.

Kalli hotunan:

Kaduna: Kwastam Ta Kama Babban Motar Maƙare Da Naman Jaki Da Ganyen Wiwi

A wani labarin, a ranar Juma’a, hukumar kwastam ta shaida yadda ta kwace wata babbar mota cike taf da naman jaki da buhunhunan kayan maye masu kimar fiye da N250,000,000 a cikin wata daya, The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yan bindiga sun kai mummunan hari Hedkwatar yan sanda, mutane sun yi takansu

Yayin tattaunawa da manema labarai a Kaduna, shugaban hukumar na Zone “B” Kaduna, Albashir Hamisu, ya bayyana yadda aka boye buhunhunan kayan maye 2,348 da dauri 126 na wasu masu kimar N251,701,000,000.

Hamisu ya bayyana hakan ne inda ya ce tsakanin ranar 24 ga watan Fabrairu da 23 ga watan Maris na shekarar 2022, sun kwace makamantan hakan sau 144.

Asali: Legit.ng

Online view pixel