Jerin bambanci 10 da ke tsakanin saida kamfanin NNPC da yin kasuwanci da NNPC

Jerin bambanci 10 da ke tsakanin saida kamfanin NNPC da yin kasuwanci da NNPC

  • A makon nan ne aka rika yada labarin cewa gwamnatin tarayya ta saida kamfanin NNPC
  • Masana su na cigaba da yin karin haske a kan wannan batu, da hakikanin abin da matakin ke nufi
  • A zahirin gaskiya har yanzu gwamnatin tarayya ke da iko da NNPC, ba a saida kamfanin ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kano - Tijjani Ahmed wanda masanin harkar tattalin arziki ne a jihar Kano, ya yi karin haske a shafinsa na Facebook a kan maganar sa NNPC a kasuwa.

Masanin malami ne a makarantar koyon aiki ta Hussaini Adamu Federal Polytechnic Kazaure a Jigawa, kwararren Akawu ne da ICAN ta san da zaman shi.

A maganar da ya yi a shafinsa, ya kawo bambanci 10 tsakanin canza salon NNPC da gwamnatin Muhammadu Buhari ta yi, da kuma a ce an saida kamfani.

Kara karanta wannan

Abba Kyari: An cigaba da shari’a, NDLEA ta gabatar da hujjojin kwayoyi da Daloli

Kwararren yake cewa yanzu Najeriya za ta maida hankali da kyau wajen yin kasuwanci ne da NNPC, akasin cewa kamfanin ya tashi daga hannun gwamnati.

Kashi 100% na hannun jarin NNPC yana hannun gwamnati da hukumominta, illa iyaka daga yanzu za a rika mu’amalantar NNPC ne kamar sauran kamfanoni.

Ahmed wanda ya yi digirinsa a jami’ar Ahmad Bello da ke Zariya, ya ce akwai yiwuwar nan gaba a saida hannun jarin kamfanin man ga wasu ‘yan kasuwan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A bayanin da ya yi, masanin ya bada misali da kamfanonin gida da waje irinsu NLNG wanda gwamnati da ‘yan kasuwa duk su ke da hannun jari a cikinsu.

kamfanin NNPC
Taron kaddamar da kamfanin NNPC Ltd Hoto: @BuhariSallauOnline
Asali: Facebook

Bayanin Tijjani Ahmed

1. NNPC anyi "Commercializing" nasa, ba privatisatizing" nasa aka yi ba.

2. Akwai banbanci sosai tsakanin "Privatization" da Commercialization"

3. "Privatisation" yana nufin sayar da kadara ko kuma kamfani mallakar gwamnati zuwa ga yan 'kasuwa.

Kara karanta wannan

Atiku yana ganin Buhari ya yi abin da ya cancanci yabo, ya jinjinawa Shugaban kasa

4. "Commercialization" yana nufin canja gudanarwar kamfani mallakar gwamnati ya koma ana gudanar da shi kamar yadda ake gudanar da kamfani na yankasuwa, ba tare da an sayar da shiba.

5. Shi NNPC Limited gwamnatice zata ci gaba da gudanar da shi saboda ita ta mallaki 100%.

6. Gudanarwar zata kasance a sabon tsari kamar yadda ake gudanar da kamfanunuwan 'yan kasuwa (domin samun riba).

7. Nan gaba kuma idan taga dama zata iya siyarwa da yan kasuwa hannun jari domin shigowa cikin gudanarwar, kamar yadda akayi a NLNG, Gwamnati tana da 49%, yan kasuwa suna da 51%. (Shell Gas B.V. suna da 25.6%, Total LNG Nigeria Ltd suna da 15% sai kuma Eni International suna da 10.4%.)

8. Misalin Saudi Aramco (Shine kamar NNPC na Saudi Arabia) gwamnatin Saudia tana da kaso 98.5% su kuma yan kasuwa suna da 1.5%.

9. Ethiopian Airline, shima commercialized company ne wanda gwamnatin Ethiopia take da 100% ownership (Kamar NNPC a yanzu) kuma take gudanar da shi domin riba.

Kara karanta wannan

Yadda matashi ya sace janareto da lasifikar Masallaci a Adamawa, ya sheke kudin a tabar wiwi

10. Akwai misalai da dama a kasashen Africa, Asia, Middle East da sauran bangarori na duniya.

Shawarar Atiku Abbakar

A jiya aka ji Atiku Abubakar ya ce Gwamnati ta yi ta sukarsa saboda kawo maganar saida NNPC a 2018, amma sai ga shi yanzu an kama hanyar bin shawararsa.

Burin Atiku Abubakar shi ne NNPC ya bi sahun kamfanin Aramco da Saudi ta saida, da irinsu Petrobras da gwamnatin Brazil ta saidawa 'yan kasar hannun jari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel