Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga farmaki jerin gwanon motocin shugaba Buhari a Katsina

Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga farmaki jerin gwanon motocin shugaba Buhari a Katsina

  • 'Yan bindiga sun far wa tawagar motocin shugaban ƙasa Buhari a kan hanyar su ta zuwa Daura a shirye-shiryen zuwa Babbar Sallah
  • Malam Garba Shehu, ya ce tawagar ta ƙunshi, hadimai, ma'aikata da yan jaridar gidan gwamnati amma Buhati baya ciki
  • Mutum na kwance a Asibiti sakamakon harin wanda gwarazan jami'an tsaro suka daƙile

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Katsina - A ranar Talatan nan, miyagun yan bindiga sun buɗe wa jerin gwanon tawagar motocin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, wuta a jihar Katsina.

A cewar mai magana da yawun shugaban, Malam Garba Shehu, mutum lamba ɗaya a Najeriya ba ya cikin tawagar lokacin harin. kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.
Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga farmaki jerin gwanon motocin shugaba Buhari a Katsina Hoto: Buhari Sallau
Asali: UGC

Jami'an tsaro da sauran yan tawagar shugaban ƙasan na kan hanyar zuwa Daura, mahaifar Buhari yayin da Babbar Sallah ke ƙaratowa, sune maharan suka farmaka a kusa da Dutsin-ma.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan Sa'kai sun yi kazamin artabu da 'yan bindiga a Filato, rayuka sama da 10 sun baƙunci lahira

Yadda lamarin ya faru

Malam Shehu ya ƙara da cewa gwarazan dakarun tsaron shugaban ƙasa sun daƙile yunkurin kai harin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jaridar Punch ta ruwaito Shehu Ya ce:

"Fadar shugaban ƙasa ta ayyana a matsayin abin takaici da ake gudu, farmakin da aka kai wa jerin gwanon motoci da ke tattare da tawaga, masu hidima da jami'an midiya kusa da Dutsin-ma a shirye-shiryen zuwan shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari Daura domin babbar Sallah."
"Maharan sun buɗe wa tawagar motocin wuta daga wasu wurare da suka yi kwantan ɓauna amma duk da haka suka kwashi kashin su a hannun Sojoji, yan sanda da dakaraun hukumar DSS da ke wa motocin rakiya."
"Mutum biyu daga cikin mutanen da ke tawagar motocin na karɓan kulawa saboda wasu ƙananan raunuka da suka ji. Baki ɗaya sauran jami'ai, ma'aikata da motoci sun isa Daura lafiya."

Kara karanta wannan

Miyagun yan bindiga sun kai hari jihar Kano, sun yi garkuwa da Basarake da wata matar aure

A wani labarin na daban kuma 'Yan bindiga sun buɗe wa masu Jana'iza wuta a jihar Kaduna

Mutane sun gano gawar Malamin Cocin ECWA wanda aka yi garkuwa da shi lokacin da yan bindiga suka farmaki kauyen Tudun Ibru a Kaduna.

Shugaban CAN na Kaduna ya ce yayin da Coci ta tafi domin masa jana'iza, yan bindiga suka sake buɗe wuta suka tarwatsa mutane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel