'Yan bindiga sun yi garkuwa da wani Basarake da matar aure a jihar Kano

'Yan bindiga sun yi garkuwa da wani Basarake da matar aure a jihar Kano

  • Wasu 'yan bindiga sun kai hari kauyen Bari a jihar Kano, sun yi awon gaba da wani mai rike da sarauta da kuma wata matar aure
  • Wani mazaunin ƙauyen da ke yankin ƙaramar hukumar Rogo, ya ce wannan ba shi ne karo na farko ba, sun shiga damuwa sosai kan lamarin
  • Sai dai da aka nemi jin ta bakin kakakin hukumar yan sandan Kano, Abdullahi Kiyawa, ya ce bai samu bayani kan harin sace mutanen ba

Kano - Wasu miyagun ƴan bindiga sun kai farmaki ƙauyen Bari, ƙaramar hukumar Rogo a jihar Kano da misalin ƙarfe 11:00 na dare kuma suka yi awon gaba da wani mai rike da Sarauta da matar aure.

Daily Trust ta ruwaito cewa mutanen da suka shiga hannun 'yan bindigan su ne, Shehu Bello Bari (Yariman Bari), ƙanin Dagacin ƙauyen Bari; da kuma wata matar aure, Binta Abdulƙadir.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun mamaye majalisar dokokin jiha a arewa bayan an yi yunkurin ƙonata

Yan bindiga sun kai hari ƙauyen Kano.
'Yan bindiga sun yi garkuwa da wani Basarake da matar aure a jihar Kano Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Wani mazaunin ƙauyen Bari, Suleiman Abdulƙadir, ya shaida wa wakilin jaridar cewa kwanakin baya aka yi garkuwa da ɗan uwan matar auren da aka sace amma daga bayan masu garkuwan sun sako shi.

Malam Abdulƙadir ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Muna cikin tsananin damuwa game da lamarin, saboda har zuwa yanzun ba bu wanda ya tuntuɓi iyalanta bare mu san halin da take ciki."

Wane mataki yan sanda suka ɗauka?

A yanzu da muke haɗa wannan rahoto, kakakin hukumar 'yan sanda reshen jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa ba shi da masaniya kan sace mutanen.

Yankin arewa maso yammacin Najeriya na fama da matsalar tsaro mai muni, wacce galibi yan bindiga ne ke kai hare-hare suna kashe jama'a da sace wasu.

Matsalar ta fi ƙamari a jihohi kamar Zamfara, Kaduna, Sokoto da Katsina, inda maharan ke kaiwa mazauna, ma'aikatan gwamnati da wuraren gwamnati hari.

Kara karanta wannan

Shiroro: Buhari ya sha alwashin ceto 'yan China da aka sace, ya hukunta 'yan ta'adda

A wani labarin kuma Wasu mayaƙan ISWAP da suka yi yunkurin kai hari Monguno sun kwashi kashin su a hannun Sojoji

Sojojin haɗin guiwa na kasa da ƙasa MNJTF na runduna ta uku sun yi nasarar daƙile mummunan harin mayaƙan ISWAP a Borno .

Masani kuma mai sharhi kan harkokin tsaro, Zagazola Makama, ya ce an kwashe fiye da a wa ɗaya ana ɗauki ba daɗi da yan ta'addan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel