Da Ɗumi-Ɗumi: Mutum 12 sun rasa rayukansu yayin da Yan Sa'kai suka gwabza da yan bindiga a Filato

Da Ɗumi-Ɗumi: Mutum 12 sun rasa rayukansu yayin da Yan Sa'kai suka gwabza da yan bindiga a Filato

  • Kusan mutum 12 ake fargabar Allah ya karɓi rayuwarsu yayin wani gurmurzu tsakanin yan bijilanti da yan bindiga a Filato
  • Wani shugaban matasa a yankin Wase, ya ce yan bindiga Tara da Yan Bijilanti uku suka mutu kuma Sojoji sun kawo ɗauki
  • Lamarin wanda ya faru a ƙauyen Zak, rundunar OPSH ta tura dakarun soji don taimaka wa yan Bijilanti

Plateau - Akalla mutane 12 ake fargabar sun rasa rayukansu a wata arangama tsakanin Yan Bijilanti da miyagun yan bindiga a ƙauyen Zak, ƙaramar hukumar Wase, jihar Filato.

Wani shugaban matasa a yankin Wase, Shapi'i, wanda ya tabbatar da lamarin, ya shaida wa wakilin jaridar Leadership cewa lamarin ya auku ne da ƙarfe 9:00 na safiyar Litinin.

Taswirar jihar Filato.
Da Ɗumi-Ɗumi: Mutum 12 sun rasa rayukansu yayin da Yan Sa'kai suka gwabza da yan bindiga a Filato Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Ya yi bayanin cewa artabun ya laƙume rayukan mutum 12, wanda ya haɗa da yan bindiga Tara da kuma 'yan Sa'kai wato yan Bijilanti guda uku.

Kara karanta wannan

Miyagun yan bindiga sun kai hari jihar Kano, sun yi garkuwa da Basarake da wata matar aure

Da yake bayyana yadda lamarin ya faru, Shugaban matasan ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Yan bindigan adadi mai yawa sun zo a kan Babura da sassafe, muna tsammanin sun kwana ne a dazukan da ke kusa da ƙauyen Zak."
"Lokacin da mutane suka ankara da zuwan 'yan bindigan ƙauyen su, nan take suka yi gaggawar sanar da rundunar Operation Safe Haven da ke sansani a Zak."
"Bayan samun labari nan take rundunar ta haɗa dakarun sojoji ta tura su yankin kuma suka yi nasarar daƙile harin da taimakon yan Sa'kai."

Rundunar OPSH ta tabbatar da lamarin

Kakakin rundunar sojin OPSH da ke kokarin tabbatar da zaman lafiya a Filato da wasu sassan kudancin Kaduna, Manjo Ishaku Takwa, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, amma bai faɗi adadin rayukan da aka rasa ba.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun dakile harin yan bindiga a jahar Plateau

Ya jaddada cewa kwamanda da sojojin da suka dalike harin, zarce wa suka yi ƙauyen Gajin Bashar domin su yaƙi wasu yan bindigan da suka kai wa mutane hari.

Manjo Takwa ya bayyana cewa dakarun sojin sun zarce kauyen ne bayan samun kiran gaggawa kan abinda ke shirin faruwa a yankin, kamar yadda This Day ta ruwaito.

A wani labarin na daban kuma Ɗan takarar shugaban ƙasa ya nesanta kansa da wani Hoto da aka ɗora shi kan daddumar Sallah

Tsohon gwamnan jihar Anambra kuma ɗan takarar shugaban kasa a 2023 ya nesanta kansa da Hoto da aka hangesa kan dardumar Sallah.

Peter Obi ya ce Hotonsa da wasu suka ɗora kan sallayar Sallah ba dai-dai bane ko da kuwa sun yi da kyakkyawar niyya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel