Rashin Imani: 'Yan bindiga sun buɗe wa masu Jana'iza wuta a jihar Kaduna

Rashin Imani: 'Yan bindiga sun buɗe wa masu Jana'iza wuta a jihar Kaduna

  • Mutane sun gano gawar Malamin Cocin ECWA wanda aka yi garkuwa da shi lokacin da yan bindiga suka farmaki kauyen Tudun Ibru a Kaduna
  • Shugaban CAN na Kaduna ya ce yayin da Coci ta tafi domin masa jana'iza, yan bindiga suka sake buɗe wuta suka tarwatsa mutane
  • Har yanzin rundunar yan sanda reshen jihar Kaduna ba fitar da wata sanarwa a hukumance game da gano gawar da dawowar yan bindiga ba

Kaduna - Mutane sun tsinci gawar wani Fasto na cocin ECWA, Rabaran Adamu Buba, wanda aka yi garkuwa da shi yayin da yan bindiga suka kai farmaki Tudun Ibru a ƙaramar hukumar Kajuru, Kaduna ranar Litinin da daddare.

Shugaban ƙungiyar kiristoci CAN reshen Kaduna, Rabaran Joseph John Hayab, ya tabbatar wa manema labarai a ruwayar Vanguard, cewa yan bindiga sun farmaki mutanen da suka je Jana'izar binne marigayin.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan Sa'kai sun yi kazamin artabu da 'yan bindiga a Filato, rayuka sama da 10 sun baƙunci lahira

Yan bindiga sun farmaki masu Jana'iza.
Rashin Imani: 'Yan bindiga sun buɗe wa masu Jana'iza wuta a jihar Kaduna Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Hayab ya ce:

"Eh dagaske na (An gano gawar Malamin Cocin) kuma lokacin da Cocin taje domi yi masa jana'iza da binne shi, yan bindiga suka sake buɗe wuta hakan ya sa mutane suka tarwatse."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoto ya nuna cewa mahara sun farmaki ƙauyen ranar Litinin da daddare, inda suka halaka mutum uku, kuma suka tattara mutane suka yi gaba da su.

Yadda Malamin Cocin ya rasa rayuwarsa

Wata majiya ta ce bayan aikata ta'addanci a kauyen, yan bindiga sun zarce kauyen Doka, inda suka sace wasu mutum 9.

A cewar majiyar:

"Masu garkuwan sun wuce kauyen Doka suka sace mutum 9. Malamin Cocin ECWA dake Tudun Ibru, Rabaran Adamu Buba, na cikin waɗan da maharan suka sace."
"Amma da safiyar nan, yayin da mutane ke bin sawun masu garkuwa da mutane suka ci karo da gawar malamin."

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun dakile harin yan bindiga a jahar Plateau

Har zuwa yanzu da muke tattara wannan rahoton, hukumar yan sanda reshen jihar Kaduna ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba game da lamarin.

A wani labarin kuma Matar shugaban ma'aikata da aka sace a Zamfara ta haihu a sansanin 'yan bindiga, ta kira shi a waya

Shugaban ma'aikatan kananan hukumomi na jihar Zamfara, Sanusi Isa, ya tabbatar da cewa matarsa ta haihu a sansanin yan bindiga.

Wasu miyagu sun kut sa har cikin gidan shugaban ƙungiyar NULGE suka yi gaba da matarsa yayin da suka gano baya nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel